Tirkashi: Wani Dalibin jami'a ya lakadawa malamarsa duka kawo wuka daga neman taimako
- Wani ɗalibin dake 400- Level a jami'ar Ilorin (UNILORIN) ya lakaɗawa malamarsa a jami'a dukan kawo wuka
- Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, lokacin da ɗalibin ya je ofishin malamar neman ta taimaka masa
- Hukumar jami'ar ta yi Allah wadai da faruwar lamarin, sannan ta sha alwashin ɗaukar matakin da ya dace
Kwara - Wani ɗalibi dake karantar kwas ɗin Microbiology a jami'ar Ilorin, (UniLorin) ya lakaɗawa lakcaransa mace dukan kawo wuka.
Dailytrust tace Ɗalibin mai suna, Captain Walz, bai samu damar yin kwas ɗin neman sanin makamar aiki ba (SIWES), dan haka yaje neman taimakon lakcaran.
Rahotanni sun bayyana cewa lakcaran da abin ya shafa, Mrs Zakaria, ita ce zata kula da ɗalibin yayin da zai yi Project a 400 level.
Hakanan kuma an tabbatar da cewa Walz ya lakadawa malamar tasa dukan tsiya ne ranar Alhamis din nan da ta gabata.
Meyasa abin ya kai da duka?
A binciken da muka yi, dalibin ya je har ofishin malamar domin neman ta taimaka masa, saboda bai samu damar yin SIWES ba kwata-kwata.
Amma da lakcaran ta nuna ƙin amincewar ta, kuma idan bakai SIWES ba ba zaka yi Project ba, nan take Walz ya fusata, ya lakaɗawa malamar dukan tsiya wanda yasa ta ji raunuka a jikinta.
Bugu da ƙari, ba'a ɗauki dogon lokaci ba aka kawo mata ɗauki kuma aka garzaya da ita asibiti domin kula da lafiyarta.
Wane mataki jami'a ta ɗauka?
Daraktan hulɗa da jama'a na jami'ar, Mr Kunle Akogun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar salula ranar Asabar da daddare.
Yace:
"Eh tabbas lamarin ya auku, amma lakcaran tana yanayi mai kyau, kuma tuni mataimakin shugaban jami'ar (VC), Farfesa Abdulkareem Age da wasu malaman jami'a suka ziyarci lakacaran da lamarin ya shafa."
"Jami'a baki ɗaya bata ji daɗin abinda ya faru ba, kuma zata tabbatar da an yi adalci. Sannan kuma ya roki a kula da lafiyar malamar yadda ya dace ta asusun jami'a."
A wani labarin kuma Sheikh Abduljabbar ya shaida wa kotu cewa ba shi da kuɗi domin tun bayan da aka tsare shi kasuwancinsa ya tsaya cak
Malamin ya faɗi haka ne yayin da yake martani ga umarnin alkalin kotun dake masa shari'a, Mai shari'a Abdullahi Sarki Yola.
Alkalin kotu ya bukaci Abduljabbar Kabara ya mallaki litattafan Hadithi kamar, Sahih Bukhari da kuma Sahihi Muslim domin kare kansa.
Asali: Legit.ng