Dukiyar Aliko Dangote ta karu da sama da Naira biliyan 800 cikin watanni 3 a 2021

Dukiyar Aliko Dangote ta karu da sama da Naira biliyan 800 cikin watanni 3 a 2021

  • Dukiyar mai kudin Afrika, Aliko Dangote ta karu da fam Dala biliyan biyu a kusan watanni uku.
  • Dangote ne kadai mutumin Najeriya da ke cikin wadanda ke sahun gaba a jerin Attajiran Duniya.
  • Daga Dala biliyan 17.8 a Agusta, ana hasashen cewa yanzu Dangote ya ba Dala biliyan 19.8 baya.

South Africa - Jaridar kasar Afrika ta kudu, Business Africa Insider tace dukiyar Alhaji Aliko Dangote ta karu sosai a karshen wannan shekarar.

Jaridar tace mai kudin na Afrika ya hankada gaba a jerin attajiran Duniya kamar yadda sababbin alkaluman Bloomberg Billionaires Index suka nuna.

Aliko Dangote ya yi gaba a rukunin masu kudin, inda yanzu ya kai matsayi na 102 a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar nan, Dangote ne na 118.

Kara karanta wannan

Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dubai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC

Business Africa Insider tace Dangote ya kara kimanin Dala biliyan biyu a dukiyarsa daga Agustan shekarar 2021 zuwa ranar 8 ga watan Nuwamban nan.

Arzikin Dangote ya kai N8tr

Hasashe ya nuna Dangote wanda ya cika shekara 64 a watan Satumba ya mallaki Dala biliyan 17.8 (Naira tiriliyan 7.33) a watanni uku da suka wuce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kawo yanzu, ana maganar dukiyar Dangote ta kai akalla Dala biliyan 19.8. Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a yau kudin sun zarce Naira tiriliyan 8.

Aliko Dangote
Aliko Dangote Hoto: time.com
Asali: UGC

Karin da aka samu a dukiyar babban attajirin ya kai Naira biliyan 800 a cikin ‘yan kwanakin.

Hakan ya sa Dangote ya samu karin matsayi har 16 tsakanin Agustan na bana da Nuwamba. Attajirin yana cikin wadanda suka fi motsawa a 2021.

Jerin masu kudin Afrka

Sauran mutanen Afrika da ke cikin manyan masu kudin Duniya bayan Dangote sun hada da attajirin nan na Afrika ta kudu, Johann Rupert da iyalinsa.

Kara karanta wannan

Dangote da MTN ne kamfanonin da suka fi biyan haraji a Nigeria, jimmilar kudin da aka samu N289.4bn

Rahoton yace ragowar su ne: Natie Kirsh, Nicky Oppenheimer da mai kudin kasar Masar. Nassef Sawiris wanda shi kadai ne ya fito daga wajen Afrika ta kudu.

Dangote wanda yake kasuwanci a kudancin Najeriya ya ba harkar siminti, sukari, mai da taki karfi.

A ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba, 2021 aka ji cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya hadu da manyan Attajiran kasar nan a kasar Saudi Arabiya.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai da hula da jama’a, Femi Adesina yace Buhari ya hada da Aliko Dangote da shugaban kamfanin BUA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng