Kotu ta hukunta saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a

Kotu ta hukunta saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a

  • Wata kotu a kasar Uganda ta yanke wa wani saurayi da budurwa hunkuncin daurin watanni 30 saboda lalata a kan titi
  • Alkalin kotun ya bayyana cewa abin da mutanen biyu suka aikata ya saba doka kuma tada hankulan mutane ne
  • Wadanda aka gurfanar din sun amsa laifinsu bayan da mai gabatar da kara ya karanto tuhumar da ake musu

Uganda - Kotu ta yanke wa wani mutum da wata mata suna jima'i a gefen titi da rana tsaka yayin da mutane suke zirga zirga hukuncin daurin watanni 30 a gidan gyaran hali a Uganda, rahoton LIB.

An kama Hafashimana Paskari, mai shekaru 29 mazaunin kauyen Migeshi, Rwaramba Parish da Muhawenimana Colodine Mukamulenzi, mai shekaru 24 a makon da ya gabata kan laifin tada hankalin mutane.

Kotu ta hukunta saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a
Kotu ta hukunta saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kotun Majistare na Kisoro a ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba ya samu mutanen biyu da aikata laifin a kan babban hanyar Kisoro zuwa Bunagana.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

Ofishin babban mai shari'a a yankin ya tabbatar da cewa abin da suka aikata ya saba doka kamar yadda ya zo a ruwayar LIB.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi zargin cewa Paskari da Colodine a ranar 2 na watan Nuwamban 2021 misalin karfe 5 na yamma a kan hanyar Kisoro sun yi jima'i a bainar jama'a, abin Allah-wadai.

Kotu ta hukunta saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a
Alkali ya hukunta saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kotu ta hukunta saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a
Kotu ta daure saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a. Hoto: LIB
Asali: Facebook

An gurfanar da su a kotu a ranar Talata a gaban Mai sharia Fred Gidudu yayin da Muhendo Peter ya gabatar da karar.

Ba su musanta aikata laifin ba

Mutanen biyu sun amsa laifinsu kuma aka yanke musu hukuncin daurin watanni 30 a gidan yari.

A wani bidiyo da ya karade dandalin sada zumunta, an gano Mukamurenzi da Paskari suna tafiya tare a gefen babban titin nan take, ba tare da gargadi ba suka yi jima'i ba tare da damuwa cewa mutane na kallonsu ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

Magidanci Ya Lakaɗa Wa Likitan Fata Mugun Duka Saboda Yaba Kyawun Fatar Matarsa

A wani labarin daban, 'yan sanda sun kama wani mutum bayan ya lakada wa likita dukan tsiya inda ya bar shi a mawuyacin hali bayan yabon kyawun fatar matar sa.

Matar wacce musulma ce mai sanye da hijabi ta sanar da mijinta, Bakhriddin Azimov cewa likitan fatar dan asalin kasar Rasha, Vladimir Zhirnokleev ya yaba kyawun fatarta.

Daga nan ne mutumin ya kai wa likitan farmaki, yanzu haka yana fuskantar hukunci akan cin zarafi kamar yadda LIB ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164