Da duminsa: Amurka za ta bude iyakokin ta bayan wata 20 da rufe su
- A yau Litinin ne kasar Amurka za ta bude iyakokin ta na tudu da na sama bayan watanni 20 da garkame su baki daya
- Tsohon shugaban kasa Donald Trump ne ya saka dokar a watan Maris na 2020 inda magajinsa Biden ya dabbaka ta
- An saka dokar ne saboda dakile yaduwar cutar korona a kasar wacce ta zama annoba sannan ruwan dare a shekarar da ta gabata
Amurka - Kasar Amurka za ta bude iyakokin ta na tudu da na sama a ranar Litinin domin bakin da suka yi cikakken riga-kafin cutar Korona, lamarin da zai kawo karshen hana baki shiga Amurka da aka yi na tsawon watanni 20.
Shugaban kasa Donald Trump ne ya saka dokar a farkon shekarar 2020 kuma wanda ya gaje shi, Joe Biden ya dabbaka ta. Jama'a da dama sun dinga sukar dokar da annobar korona ta ja aka kakaba.
Wannan dokar ba a tsawwala su ba a Turai da makwabtan Amurka ba irin su Canada da Mexico, Daily Trust ta wallafa.
A kokarin dakile yaduwar cutar korona, Amurka ta rufe iyakokin ta bayan watan Maris na 2020 daga matafiyan da ke tahowa daga manyan sassan duniya da suka hada da Kungiyar hadin kan Turai, Birtaniya da China, Indiya da Brazil. Baki da ke shiga kasar a kasa ta Mexico da Canada duk an hana su.
A watannin da aka saka dokar hana shiga kasar, miliyoyin mutane sun fada wahala a fannin al'amuransu na yau da kullum kuma an sha wahala kan matsalar tattalin arziki da annobar ta kawo.
"A gaskiya babu sauki," Alison Henry mai shekaru 63 ta sanar da AFP. "Ina son ganin da na ne."
Matar 'yar kasar Birtaniya ta shirya shiga kasar a ranar Litinin domin ganin dan ta a New York bayan wata 20 da aka raba su.
Iyalai daga dukkanin bangarorin kogin Atlantika sun kosa su hadu da masoyansu, Daily Trust ta wallafa.
Bawan Allah ya siya jirgin sama, ya mayar da shi gida da bandaki, bidiyon ya bada mamaki
A wani labari na daban, ba kamar jama'a da je zama a gidaje ginannu ba, wani mutum ya yanke shawarar zama cikin jirgin sama.
Dan asalin kasar Amurkan mai suna Bruce Campbell ya siya jirgin da aka kera tun a shekarar 1969 a 1999 a kan farashi $100, 000 (N41 million).
A kokarin Bruce na mayar da jirgin saman yadda ya ke so, ya sake kashe wasu kudi har $120, 000 (N49 million) domin gyara shi bayan ya mayar da shi wani filin shi da ke Portland.
Asali: Legit.ng