'Karin bayani: Adadin wadanda suka mutu a gobarar kasuwar Abuja ya ƙaru zuwa 7

'Karin bayani: Adadin wadanda suka mutu a gobarar kasuwar Abuja ya ƙaru zuwa 7

  • Adadin mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar Kubwa, Abuja ya karu zuwa 7
  • A jiya Juma'a ne misalin karfe 7 na dare gobarar ta tashi bayan fashewar wani tanki da ke dauke da kalanzir a gaban shago da ke kusa da kasuwar
  • Wani jami'i a babban asibitin Kubwa da ke Abuja, a safiyar ranar Asabar ya tabbatar da mutuwar a kalla mutane 7 da ya gawarsu na ajiye a asibitin

FCT, Abuja - Adadin wadanda suka rasu sakamakon gobarar kasuwar Abuja a daren ranar Juma'a ya karu daga uku zuwa bakwai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gobarar ta tashi ne daga wani tankin kalanzir da ke ajiye a gaban wani shago da ke kallon kasuwar ta zamani na Kubwa misalin karfe 7 na dare.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

Bayan fashewar tankin kalanzir din, tankar da ke dauke da kalanzir din ta daka tsale daga inda ta ke ta fada kan rufin wasu gine-gine da ke kusa.

'Karin bayani: Adadin wadanda suka mutu a gobarar kasuwar Abuja ya ƙaru zuwa 7
Rufin gidan da tankin kalanzir din ya yi tsalle ya fada a kai. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ganau, Ebuka Okonkwo, wanda ya ce ya garzaya wurin bayan jin karar fashewar ya gano mutane suna ta fadi a kan juna a yayin da suke kokarin tserewa.

Ya ce:

"Daga nan ne naga wasu mutane suna konewa, ciki har da wata mata da yar ta."

Wakilin Daily Trust da ya ziyarci wurin a safiyar ranar Asabar ya ce a kalla shaguna bakwai da suka gefen titi sun kone.

Wani ma'aikacin asibiti a babban asibitin Kubwa inda aka kai wasu da abin ya shafa ya ce kawo yanzu an kai gwarwaki bakwai wurin ajiyar gawa na asibitin.

Na rasa 'yan uwa na su biyar, Boniface

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto malaman UNIAbuja da aka sace, an kama 'yan bindiga

Wani mutum mai suna Echefo Boniface wanda aka gan shi tare da wasu mutane da ke jimamin rashin yan uwansu a gaban dakin ajiye gawarwaki a asibiti ya ce ya rasa mutum biyar daga kauyensa na Abajah a karamar hukumar Nwangele, Imo.

Ya ce cikin wadanda suka mutu akwai mata mai juna biyu, uwa da yar ta, sai yara mata guda biyu masu shekaru 10 da 16.

Ya ce an tura daya daga cikinsu babban asibitin Abuja amma ta mutu a hanyar kai ta asibitin.

Aliyu Sabo, wani mai sayar da yayan itatuwa a kusa da abin ya faru yace ya tsere bayan jin sautin mai karfi.

Rahotanni sun ce a kalla mutane tara sun samu munanan rauni kuma har yanzu suna asibiti ana basu kulawa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel