Fitattun 'yan Najeriya 5 da ke jan ragamar shugabancin wasu manyan hukumomin duniya
Najeriya kasa ce da ke da albarkatun kasa masu dimbin yawa baya ga hakan Allah ya albarkaci kasar da mutane da ke yin ayyuka da dama a fadin duniya.
A wannan rahoton, The Nation ta kawo jerin wasu 'yan Nigeria da ke jagorantar wasu hukumomi na duniya wanda hakan yasa 'yan Nigeria na alfahari da su.
1. Amina Jane Mohammed
An haife ta ne a kasar Birtaniya, mahaifinta Hausa/Fulani ne yayin da mahaifiyarta ma'aikaciyar jinya ne a Burtaniya.
Ta rike mukamin ministan muhalli a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2017.
A Janairun 2017, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antoni Guterres ya sanar da niyyarsa na nada Mohammed a matsayin mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya.
Tun lokacin ta cigaba da yin ayyukanta yadda ya dace tare da bai wa kowa sha'awa.
2. Ngozi Okonjo-Iweala
Ngozi Okonjo-Iweala ce mace ta farko kuma 'yar Afirka da aka nada a matsayin shugaban kungiyar kasuwanci ta duniya, WTO.
Mrs Okonjo-Iweala ta yi aiki a matsayin Ministan Kudi a karkashin shugabannin kasa Obasanjo da Goodluck Jonathan.
Kazalika, tana rike da mukami da kwamitin direktoci a kamfanoni fiye 500 a kungiyoyin babban bankin duniya.
3. Akinwumi “Akin” Adesina
Akinwumi tsohon Ministan Aikin Noma ne karkashin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.
Ya yi karatun digirinsa na farko a bangaren tattalin arzikin aikin noma daga jami'ar OAU.
An zabe shi a matsayin shugaban bankin cigaban nahiyar Afirka a 2015, an sake zabensa a karo na biyu a 2020.
Shine dan Nigeria na farko da ya fara rike mukamin.
4. Dr. Chikwe Ihekweazu
An nada tsohon shugaban cibiyar dakile cutattuka masu yaduwa, NCDC, Dr. Chikwe Ihekweazu a matsayin mataimakin DG na tattara bayannai na lafiya a Kungiyar Lafiya ta Duniya, WHO.
Nadin ya zo ne bayan irin jagoranci na gari da ya yi a Nigeria yayin bullar annobar coronavirus.
Ya samu horaswa a matsayin mai bincike ga cutattuka masu yaduwa kuma ya shafe kimanin shekaru fiye da 20 yana aiki a matakai da dama a hukumomin lafiya.
5. HE Mohammad Sanusi Barkindo
Muhammad Sanusi shine babban sakataren kungiyar kasashe masu albarkatun man fetur, OPEC.
Asalinsa mutumin Yola ne daga jihar Adamawa. Ya yi karatun digiri a harkar kimiyyar siyasa daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Ya rike mukamai da dama a hukumomin gwamnatin jihohi da tarayya ciki har da NNPC kafin a nada shi mukamin a OPEC.
An fitar da jerin Musulmi 500 mafi ƙarfin faɗa aji a duniya, Buhari, Ɗangote, Ɗahiru Bauchi da Zakzaky na ciki
A baya, kun ji cewa Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari yana cikin jerin musulmin duniya 500 mafi karfin fada aji kamar yadda cibiyar nazarin addinin Islama da ke Amman a Jordan ta fitar.
A kowane shekara cibiyar tana fitar da sabbin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya.
Shugaba Buhari ne mutum na 16 a cikin jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya a bana kamar yadda The Muslim 500 ta fitar.
Asali: Legit.ng