Hotunan Amarya da Ango da suka je wurin ɗaura aurensu a cikin tukunyar girki

Hotunan Amarya da Ango da suka je wurin ɗaura aurensu a cikin tukunyar girki

  • Wasu sabbin ma'aurata sun yi amfani da tukunyar girki wajen zuwa ɗaura aurensu saboda ambaliyar ruwa
  • Hotunan da suka mamaye kafafen sada zumunta sun nuna yadda ma'auratan suka shiga tukunyar domin ruwa ya mamaye titunan yankinsu
  • Amarya tace ba ta yi tsammanin bikinsu zai ƙayatar haka ba, amma yanzun ba zasu taba mantawa ba

India - Bisa tilas wata amarya da angonta suka yi amfani da tukunyar girki wajen tsallake wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye yayin zuwa wurin ɗaura aurensu a ƙasar Indiya.

Hotunan waɗannan ma'aurata ya ƙaraɗe kafafen sada zumunta domin sun yi abin mamaki kasancewar ambaliyar ruwa ta mamaye tituna a gabashin Indiya.

BBC Hausa ta rahoto cewa Amaryar da Angonta sun ɗauki wannan matakin ne saboda ambaliyar da ta shafi yankinsu.

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

Amarya da Ango
Hotunan Amarya da Ango da suka je wurin ɗaura aurensu a cikin tukunyar girki Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Angon mai suna Akash, da kuma amaryarsa, Ashwarya, sun sha alwashin tabbatar da an ɗaura auren su duk da wannan matsala da suke fama da ita a ƙauyensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ya suka yi amfani da tukunya?

Hotunan sabbin ma'auratan, waɗan da ma'aikatan lafiya ne, sun nuna yadda suka zauna daram a cikin tukunya domin wuce wuraren da ruwan ya mamaye.

Rahotanni sun bayyana cewa ruwan sama mai ƙarfi ya haifar da ambaliya a yankin jihar Kerala, mutane sun mutu da dama.

Ma'auratan sun nemo tukunyar ne a wurin Bauta, sannan suka nemi taimakon wasu mutane da zasu rinka tura su tamkar kwale-kwale.

Amarya da Ango
Hotunan Amarya da Ango da suka je wurin ɗaura aurensu a cikin tukunyar girki Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Ba zamu taba mantawa da wannan lokacin ba - Ashwarya

Amaryar ta bayyana cewa sam ba su yi tsammanin bikinsu zai kai haka ba, domin ya wuce duk wani tunanin su.

Amaryar tace:

"Da fari mun tsara bikin mu da mutane yan kaɗan, amma sai ga shi ya kasance bikin da ba zamu iya mancewa da shi ba."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Ɗan Majalisar Dokoki a Najeriya

Amarya da Ango
Hotunan Amarya da Ango da suka je wurin ɗaura aurensu a cikin tukunyar girki Hoto: thequint.com
Asali: UGC

A wani labarin kuma Wani matashi ya hallaka ɗan shekara 50 da ya kama a dakin budurwarsa suna biɗala

Rahoto ya nuna cewa mutanen biyu suna neman mace ɗaya, inda shi matashin ya kama ɗayan a ɗaki , yasa wuka ya sare shi.

Kakakin yan sanda, Abimbola Oyeyemi, yace matar da ake rigima a kanta ta tsere ba'a san inda take ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262