Jerin sunayen jihohin Najeriya 12 da UK ta shawarci 'yan kasar ta da su kiyaya
- Gwamnatin Ingila ta ja kunnen 'yan kasar ta da su kiyaye kai ziyara jihohi 12 na Najeriya
- Gwamnatin ta ce ana yawan sace bakin haure a jihohin, a wasu lokutan a kai musu farmaki
- Daga jihohin akwai Kaduna, Bauchi, Borno, Legas, Cross Rivers, Katsina, Zamfara da sauransu
Ingila ta ce 'yan Boko Haram sun fi son sace wadanda ba 'yan kasar nan ba inda suka ja kunnen 'yan kasar su da tafiye-tafiye zuwa jihohi 12 na Najeriya.
Kamar yadda ofishin FCDO na Ingila ya sanar a ranar Juma'a, Ingila ta ja kunnen 'yan kasar ta tare da basu shawara kan inda ya dace su je, TheCable ta ruwaito.
Gwamnatin Ingila ta ce akwai akwai babbar barazanar cewa ana iya sace mutane a fadin Najeriya saboda a karba kudin fansa ko kuma saboda siyasa.
"Kungiyoyin tun baya sun nuna niyya da kuma kwarewa wurin satar jama'a a Najeriya. 'Yan kasashen waje da suka hada da masu aikin tallafi ne suka zama wadanda miyagun suka fi hari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wuraren tallafi da ma'aikatansu ne aka fi kai wa farmaki a arewa maso gabas da suka hada da Monguno da ke jihar Borno," shawarar ta ce.
"Akwai manyan kalubalen garkuwa da mutane a fadin Najeriya. Akwai yuwuwar ta'addanci ne suke assasa garkuwa da mutane kuma hakan zai yuwu saboda neman kudi ne ko kuma wasu burikan siyasa.
“Tsarin tsaron yankin arewa maso gabas ya tagayyara tun shekarar 2018 kuma lamarin na cigaba da karuwa.
"Akwai rahotannin da ke bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram da na ISWA su na cigaba da sace bakin haure. Har ila yau, miyagun na zama a jihohin arewaci da suka hada da Bauchi, Gombe, Kano, Kogi, Kaduna, Neja da Adamawa.
"Don haka idan za ka kai ziyara jihohin nan ko kuma ka na aiki, ku kasance masu kiyayewa gudun masu satar jama'a," gwamnatin ta ja kunne.
TheCable ta ruwaito cewa, gwamnatin UK ta shawarci 'yan kasar ta kan su kasance masu kiyaye kai ziyara jihohin Legas da Abuja domin kuwa shekara daya kenan da yin zanga-zangar EndSARS.
Ga jerin sunayen jihohin 12 na Najeriya:
Adamawa
Gombe
Kaduna
Katsina
Zamfara
Delta
Bayelsa
Rivers
Akwa Ibom
Cross River
Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda
A wani labari na daban, a kalla rayuka 12 aka kashe yayin farmakin da 'yan bindigan daji suka kai kauyen Sakajiki da ke masarautar Kauran Namoda a jihar Zamfara.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a.
Ya ce an samu wadanda suka rasa rayukansu yayin aukuwar lamarin kuma ba don taimakon jami'an tsaro ba, da abun ya fi haka muni.
Asali: Legit.ng