Kamfanin Apple ya cire manhajar Al-Kur'ani a 'Apple Store' a kasar China
- Kasar China ta bukaci kamfanin Apple da ya cie wasu manhajoji daga ma'ajiyar ga mutanen kasar
- A halin yanzu, an cire manhajar Al-Kur'ani ta Qur'an Mujaheed ga mazauna kasar ta China
- Wanda ya kirkiri manhajar ya ce, manhajar tasa ta saba dokoki da ka'idojin kasar China, wannan yasa aka cire ta
China - BBC ta ruwaito cewa, kamfanin Apple ya cire manhajar Quran Majeed, shahararriyar manhajar karatu da sauraron Al-Kur'ani, daga ma'ajiyarsa ta 'Apple Store' ga mutanen China.
An ruwaito kamfanin ya cire manhajar ne bisa bukatar bukatar jami'an gwamnatin kasar China.
Ana samun manhajar Quran Majeed kyauta kuma manhaja ce da musulmai sama da miliyan 25 ke amfani da ita a duniya, inji wanda ya kirkiri manhajar.
Cire manhajar da alama ba shi da alaka da abin da ke ciki na addini, a cewar Apple, an cire ta ne saboda tana kushe da abubuwan da suka saba dokar China, kamar yadda wanda ya kirkiri manhajar ya fada.
Wanda ya kirkiri manhajar ya kumace, yana kokarin warware matsalar tare da Hukumar Intanet ta China.
Rahoton CBC ya kara da cewa, ba iya manhajar Al-Kur'ani aka cire daga ma'ajiyar manhajojin Apple na mutanen China ba, har da wata manhajar littafin Injila.
Kasar China na daya daga cikin kasashen duniya da ke ta tsaro mai karfi kan abubuwan da suka shafi Intanet, inda ake lura da tace bayanan da ke shiga da fita a kafafe da dandamali.
Bidiyon limamin Makkah na kira a daidaita sahu, karon farko sama da shekara guda
A kasar Saudiyya kuwa, tun bayan da annobar Korona ta bullo, kasashe da yawa suka shiga bin ka'idojin kariya da dama don dakile yaduwar cutar.
Kasar Saudiyya, kasa mai karbar baki masu ibadar aikin Hajji da Umarah ba a barta a baya ba, ta kasance kasar ta sanya takunkumin Korona a kokarinta na dakile yaduwar cutar.
A kwanakin baya, kasar Saudiyya ta sanar da dage dokar tazara tsakanin masallata a masallacin Harami, inda tuni dokar ta fara aiki.
Asali: Legit.ng