Bidiyon limamin Makkah na kira a daidaita sahu, karon farko sama da shekara guda
- Kasar Saudiyya ta yi watsi da dokar Korona, inda tace za a ci gaba da sallah ba tare da tazara ba
- A cikin wani bidiyo, an ga wani limami yana kira ga mamu su daidaita sahu, su hade kafadu su kuma cike gibi
- Wannan kenan a karon farko bayan da kasar Saudiyya ta dauki matakan kariya na annobar Korona
Saudiyya - Tun bayan da annobar Korona ta bullo, kasashe da yawa suka shiga bin ka'idojin kariya da dama don dakile yaduwar cutar.
Kasar Saudiyya, kasa mai karbar baki masu ibadar aikin Hajji da Umarah ba a barta a baya ba, ta kasance kasar ta sanya takunkumin Korona a kokarinta na dakile yaduwar cutar.
A kwanakin baya, kasar Saudiyya ta sanar da dage dokar tazara tsakanin masallata a masallacin Harami, inda tuni dokar ta fara aiki.
A cikin wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta samo a shafin Haramain Sharifain na Facebook, an limamin masallacin Harami yana kira da a daidaita sahu, a hada kafadu da kuma cike gibi.
Rubutun da ke dauke da bidiyon ya ce:
"Bayan shekara daya da rabi… Sheikh Baleelah yayi kira da a daidaita sahu, a cike gibi."
Kalli cikakken bidiyon:
Za'a daina bada tazara a sahun Sallah daga gobe Lahadi a Makkah da Madina
A tun farko, Hukumomi a Masallatai biyu mafi daraja a duniya zasu yi watsi da dokar wajabta baiwa juna tazara yayin Sallah a Masallacin Haram dake Makkah da Masjid Al Nabawi dake Madina.
Za'ayi yi watsi da wannan doka ne fari daga ranar Lahadi, 17 ga watan Oktoba, 2021.
Sheikh AbdulRahman Sudais ne shugaban Masallatan Biyu.
Wata majiya a fadar Sudais ta bayyana cewa za'a cire dokar bada tazaran ne daga ranar Asabar bayan Sallar Isha, rahoton Haramain Sharifain.
Hakazalika a daren nan za'a fara cire sitikun da aka manna a kasa don bayyana sahu.
Asali: Legit.ng