Da Dumi-Dumi: Dan Majalisar Dokoki Ya Rigamu Gidan Gaskiya Bayan Caccaka Masa Wuka a Mazabarsa

Da Dumi-Dumi: Dan Majalisar Dokoki Ya Rigamu Gidan Gaskiya Bayan Caccaka Masa Wuka a Mazabarsa

  • Ɗan majalisar dokoki a ƙasar Birtaniya, David Amess, ya rigamu gidan gaskiya jim kaɗan bayan kai masa hari da wuka a mazaɓarsa
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Mista Amess ya rasa ransa ne yayin da yake ganawa da mutanen da yake jagoranta a mazabarsa
  • A halin yanzu, jami'an yan sandan ƙasar sun samu nasarar damke wani mutum ɗaya da ake zargin shine ya aikata lamarin

United Kingdom - Wani ɗan majalisar dokokin Birtaniya, David Amess, ya rasa rayuwarsa sanadiyyar caka masa wuka ba sau ɗaya ba a mazaɓarsa.

BBC Hausa ta rahoto cewa wasu mutane sun farmaki ɗan majalisar ne yayin da yake ganawa da mutanen da yake wakilta a mazaɓarsa.

David Amess
Da Dumi-Dumi: Dan Majalisar Dokoki Ya Rigamu Gidan Gaskiya Bayan Caccaka Masa Wuka a Mazabarsa Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta gano cewa marigayi ɗan majalisan yana jagoranci ne ƙarƙashin inuwar jam'iyyar 'Conservative' mai mulki.

Hakanan kuma marigayi David Amess ya kasance a majalisar dokokin ƙasar Burtaniya tun a shekarar 1983.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Jirgin Yakin Rundunar Soji Ya Yi Hatsari a Kan Gidajen Mutane, Da Yawa Sun Mutu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Bayan kai masa farmaki tare da daɓa masa wuka a jikinsa, rahotanni sun tabbatar da cewa Amess ya riga da ya mutu.

A halin yanzu jami'an yan sandan ƙasar sun damƙe wani mutum ɗaya da ake zargin yana da hannu a lamarin.

An tabbatar da mutuwar Al-Barnawi, shugaban ISWAP

Babban hafsan tsaro a Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya tabbatar da mutuwar shugaban ƙungiyar ta'addanci ISWAP, Al-barnawy.

A jawabinsa, Irabor yace:

"Ina tabbatar muku da cewa Abu Mus'ab Al-Barnawy ya mutu. Kuma kamar yadda kuka jin nan ya mutu to ya mutu."

A rahoton dailytrust, Al-Barnawy, shine ɗan tsohon shugaban ƙungiyar Boko Haram, Muhammad Yusuf, wanda jami'an tsaro suƙa kashe a shekarar 2009.

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa Wata kotu ta yanke wa wani mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama shi da laifin hallaka matarsa

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Ɗan Majalisar Dokoki a Najeriya

Mutumin mai suna, Aminu Inuwa, ya musanta abinda ake zarginsa da shi, a cewarsa sam ba shine ya kashe matarsa ba.

Amma masu gabatar da ƙara sun tabbatar da cewa shi ya aikata ƙisan bayan wani sa-insa ya haɗa shi da matar a ɗakin girki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262