An biya dan Najeriya diyyar N17m bayan abokin aikinsa ya kira shi da goggon biri a Ireland
- Kotun kwadago ta kasar Ireland ta umarci wani kamfani da ya biya dan Najeriya diyyar N17 miliyan kan cin zarafi
- Hakan ya biyo bayan cin zarafin da abokin aikinsa ya yi masa kuma ya kira sa da goggon biri har sau biyu
- Ba nan abokin aikinsa ya tsaya ba, ya tirsasa dan Najeriyan ya yi kukan biri tare da rawan biri a gaban abokan aikinsa
Ireland - CPL Solutions Ltd, wani kamfanin kasar Ireland an ci su tarar €30,000 wanda ya yi daidai da N17 miliyan ga wani dan Najeriya mai suna Kings Oluebube kan kalaman banbancin launin fata da abokin aikinsa ya yi mishi.
Kamar yadda The Irish Times ta ruwaito, Oluebebe ya na aiki a ma'ajiyar kamfanin kuma ya yi ikirarin cewa a karshen watan Fabrairun 2019, shugabansa ya kira sa da goggon biri tare da tirsasa shi ya yi kukan biri da rawan shi a gaban sauran ma'aikatan.
Ya ce, bai kai rahoton wannan cin mutuncin ba a lokacin. A cewarsa, shugabansa ya sake maimaita wannan al'amarin a gaban sauran ma'aikatan a ranar 21 ga watan Mayun 2019.
Oluebebe ya kai karar wannan cin mutunci gaban manajansu wanda ya sanar da kamfanin CPL Solutions.
Kamfanin wanda ke kasuwanci a matsayin Flexsource Recruitment, ya duba zargin inda aka tura wa shugabansa jan kunnen karshe.
Oluebebe ya bukaci bayanin sakamakon binciken a rubuce.
A martanin, ma'aikaciyar CPL wacce ta yi binciken lamarin, ta ce za ta so sanar da cewa kamfanin Flexsource ba ta goyon bayan abinda ya faru tsakanin Oluebebe da abokan aikinsa.
A hukuncin shugaban kotun kwadago, ya ce dole ne a biya Oluebebe diyya daidai da irin barnar da aka yi masa ganin cewa babbar hantara da cin mutunci aka masa.
Haugh ta ce CPL Solutions ba ta dauka wani mataki ba domin janye wannan cin mutuncin da aka yi wa Oluebebe.
A don haka aka umarci kamfanin da ya biya Oluebebe kudi har miliyan goma sha bakwai wanda ya kai albashinsa na makonni 63 ga Oluebebe kan banbancin launin fata a karkashin dokokin daukan aiki.
Kaduna: 'Yan bindiga sun sako 3 daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da suka sata
A wani labari na daban, uku daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da aka sace na Christ the King Major Seminary a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna sun samu 'yancinsu.
Kamar yadda Daily Trust ta ruiwaito, shugaban makarantar, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da sakin su da aka yi a daren Laraba.
Ya ce cocin za ta cigaba da addu'a tare da fatan a sako sauran daliban da ke hannun masu garkuwa da mutanen.
Asali: Legit.ng