Sharif Lawal
8047 articles published since 17 Fab 2023
8047 articles published since 17 Fab 2023
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kira shi yayin takaddamar EFCC, inda ya yi masa alkawarin zaɓe cikin adalci.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar zama shugaban kasa.
NHRC ta bukaci gwamnati ta kama tare da gurfanar da Sheikh Yahaya Jingir bisa zargin kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a gabanin zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan Katsina Dikko Radda ya karɓi ’yan siyasa da magoya baya daga PDP da ADC da suka koma APC a Safana, yayin da ake samun sauye-sauyen siyasa.
Tarayyar Turai ta musanta rahotannin cewa ta ƙi gayyatar INEC na sanya ido kan zaɓen shekarar 2027, tana mai cewa za ta tura ƙwararrun masu sa ido.
Ana matsa wa tsohon Gwamnan Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya fice daga APC zuwa PDP domin ya taimaka wa Ali Isa Pantami a zaɓen shekarar 2027.
Tsohon Ministan Muhalli Mohammed Hassan Abdullahi ya kalubalanci sakamakon zaɓen fidda gwani na ADC a Nasarawa, inda kotu ta sanya ranar 29 ga Satumba.
Ƙungiyar G-100 ta shirya taron haɗin kan jam’iyyun adawa a Abuja ranar 18 ga Agusta 2026 domin ƙarfafa haɗin gwiwa gabanin zaɓen 2027 da ke tafe.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya kamata a dora alhakin kashe mutanen da aka yi a a Gabas ta Tsakiya kan kasar Jamhuriyar Iran.
Sharif Lawal
Samu kari