Sharif Lawal
6194 articles published since 17 Fab 2023
6194 articles published since 17 Fab 2023
Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ba ta da shirin rusa babban masallacin Ilesa saboda aikin titin hanya.
An yi ikirarin cewa shugabar kotun daukaka kara mai shari'a Monica Dongban-Mensem tace an ba alkalan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na 2023 cin hanci.
Majalisar dattawa ta bayyana cewa shugaban kasa bai gabatar da bukatar siyo sabon jirgi a gabanta ba. Shugaban majalisar ya ce za su amince da bukatar.
Hedkwatar tsara ta kasa (DHQ) ta bayyana nasarar da dakarun sojojin Najeriya suka samu kan 'yan ta'adda daga watan Afirilu zuwa watan Yunin shekarar 2024.
Lauyan da ke wakiltar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a shari'ar da yake yi da hukumar EFCC, ya bukaci kotu ta amince ya daina wakiltarsa.
Ofishin kula da basussuka (DMO) ya bayyana basussukan da ake bin kasar nan. DMO ya ce a cikin wata uku na farkon 2024, Najeriya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 7.7.
Mataimakin shugaban jam'iyyar Labour Party (LP), Ayo Olorunfenmi, ya bayyana cewa a jam'iyyar ne kadai Peter Obi zai samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2027.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi sun samu nasarar dakile wani hari da 'yan ta'addan kungiyar IPOB suka kai wani ofishinsu. Sun hallaka biyar daga cikinsu.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa a shirye shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yake domin kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Sharif Lawal
Samu kari