Sharif Lawal
6191 articles published since 17 Fab 2023
6191 articles published since 17 Fab 2023
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmi bai da ikon nada kowa a idon doka. Ta ce hakan ya sanya za ta yiwa doka gyara a jihar.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu addu'a.
Fadar Sarkin Musulmi ta fito ta yi magana kan batun rikicin da ake yadawa tana yi da gwamnatin Sokoto. Fadar ta ce babu wata rigima a tsakanin bangarorin biyu.
Majalisar wakilai ta yi zargin cewa 'yan ta'addan da suka kai harin bam a jihar Borno ba daga jihar suke ba. Majalisar ta ce an dauko hayar su ne daga waje.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Benue sun kai samame a wani sansanin 'yan bindiga da ke jihar. 'Yan sandan sun yi nasarar hallaka wasu tare da kwato makamai.
Wasu daga cikin manyan jami'o'in Najeriya na karkashin jagorancin mata. Farfesa Aisha Sani Maikudi ita ce mace ta baya-bayan nan da za ta shugabanci jami'a.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wata Hajiya 'yar jihar Neja a kasa mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024. Ta rasu ne a birnin Makkah.
An zargi jami'an rundunar sojojin saman Najeriya da lakadawa ma'aikatan kamfanonin wutar lantarki dukan tsiya a Legas. Sun yi hakan ne bayan an datse musu wuta.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta a jihar Rivers (RSIEC) ta sanya ranar da za ta gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi 23 da ake fadin jihar.
Sharif Lawal
Samu kari