Sharif Lawal
6182 articles published since 17 Fab 2023
6182 articles published since 17 Fab 2023
Mataimakin shugaban majalisar wakilan Najeriya ya tarbi 'yan adawa da suk asauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Abia. Ya yi musu marabar shigowarsu APC.
Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hari kan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda masu yawa tare da lalata makamai masu yawa.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi kan rashin da ya yi na wasu daga cikin iyalansa.
Jami'an hukumar DSS sun samu nasarar kai wani harin kwanton bauna a kan tantiran 'yan bindiga a jihar Neja. Jami'an na DSS sun sheke wasu tare da kwato makamai.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan kuskuren da jami'an tsaro suka yi wajen jefa bama-bamai kan fararen hula a kauyukan Sokoto.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'adda masu kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar nan. Sun hallaka miyagu tare da cafke masu aikata laifuka.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wani limamin cocin Anglican tare da iyalansa a jihar Ondo. Sun bukaci a ba su makudan kudaden fansa.
An samu tashin wata mummunar gobara a jihar Nasarawa. Gobarar ta tashi ne a wata fitacciyar kasuwa inda ta lalata shaguna da kayayyaki na miliyoyin Naira.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi magana kan jirage marasa da matuka da 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka fara amfani da su wajen kai hari a fagen daga.
Sharif Lawal
Samu kari