Bola Tinubu yayi tsokaci game da Littafin tarihin Buhari

Bola Tinubu yayi tsokaci game da Littafin tarihin Buhari

Bola Ahmed Tinubu yayi dan sharhi a cikin littafin Tarihin Shugaba Muhammadu Buhari

A Jiya ne wani Bature, Farfesa John Baden ya kaddamar da littafi a game da Tarihin Shugaba Buhari

Bola Tinubu ya bayyana yadda Muhammadu Buhari ya zama Shugaban Kasar Najeriya a littafin

 

Bola Tinubu yayi tsokaci game da Littafin tarihin Buhari

 

 

 

A jiya, 3 ga watan Oktoba, Farfesa John Baden, wani masanin huldar Kasa-da-Kasa, kuma wanda yayi fice a Najeriya ya kaddamar da littafin da ya rubuta a game da Muhammadu Buhari. Farfesa Baden yana da ilmi game Najeriya da kuma Shugabannin na ta.

A littafin, marubucin ya kawo labarin yadda Muhammadu Buhari yayi gwagwarmaya, ya kuma yi wa Kasa hidima, har ya zama Shugaban Kasa. Baden ya kuma kawo yadda rayuwar Shugaba Muhammadu Buhari ta ke a gida. Farfesa Baden ya kasa wanna littafi na sa har gida 3, tare da kashi 24.

KU KARANTA: Kwanakin APC sun zo karshe inji Kure

Janaral TY Danjuma ne yayi ta’alikin wannan littafi, ko dai can TY Danjuma maigidan Buhari ne a gidan Soja, kuma abokin sa ne kwarai. Janar Danjuma mai ritaya yace ba shakka Buhari ya shiryawa mulkin Kasar nan. A cikin littafin an kawo yadda su Tinubu suka kafa Jam’iyyar APC. Wajen hada wannan Jami’yya ta mu-zo-mu-gama an yi gagwarmaya kwarai, kuma an sadaukar da kai. Har aka zabi Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar Shugaban Kasa.

Bola Tinubu wanda jigo ne a APC ya kuma yi bayanin yadda Farfesa Yemi Osinbajo ya zama Mataimakin Shugaban Kasar nan. Tinubu yace Osinbajo ya rike masa Kwamishina lokacin yana Gwamna, Farfesan shari’a ne kuma Fasto na daya daga cikin Cocin da suka fi kowane girma a Najeriya, hakan zai sa masu kallon Buhari da wata fuska su daina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel