Kada Ku Sake kuce Zakuyiwa Tinubu Zagon Kasa Ko Yankan Baya, MURIC Ga Gwamnonin Arewa

Kada Ku Sake kuce Zakuyiwa Tinubu Zagon Kasa Ko Yankan Baya, MURIC Ga Gwamnonin Arewa

  • Kungiyar MURIC Dai Ana Ganin Itace Gaba-gaba wajen ganin an tabatar da takarar Musulmi da Muslmi
  • Kungiyar MURIC ta goyi bayan Takarar Bola Da Kashim A Zaben 2023
  • Yakamata ai dokar sanya tufafi a wani sako da kungiyara MURIC ta Aikewa Da Majalissar Kasa

Lagos: Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi kira ga wasu gwamnonin Arewa da ake zargin suna shirin yi wa Atiku Abubakar aiki don ya kayar da Bola Tinubu da su daina ko su dakatar da shirin.

Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, ta hannun babban daraktan ta Farfesa Ishaq Akintola, ta ce babu wata mafita a yanzu face a marawa Tinubu baya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fitar, kuma jaridar PMnewsnigeria ta samu. A cikin sanarwa kungiyar tace:

Kara karanta wannan

2023: Ya zama wajibi dukkan Musulmi ya zabi Tinubu, inji wata kungiyar Musulmai

“Wasu gwamnonin Arewa ana zarginsu da su yi wa Alhaji Atiku Abubakar aiki. kamar yadda muka samu labari"
“Mun amince da yadda wasu gwamnonin arewa su 12, suka kudiri niyya tare da yunkurin ganin sai Ahmed Bola ya zama shugaban Nigeria. da kuma yadda suke kokari kamar yadda ya bayyana a gare mu,. ya kamata ace su dore tare da jajircewa a kan hakan."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan Za'a iya tunuwa dai MURIC a cikin wata sanarwar da rabawa manema labarai a ranar 11 ga Yuni 2022, mai taken 'MURIC Tayi Tunutuba Kuma Ta Goyi Bayan Tinubu' ta yaba wa gwamnonin Arewa goma sha biyu saboda dagewarsu da kuma yunkurin su na tabbatar da an samar da dan takara mataimaki musulmi daga yankin arewa.

Professor Ishaq Akintola
Kada Ku Sake kuce Zakuyi Tinubu Zagon Kasa Ko Aiki A Boye Inji MURIC Hoto: PMNewsNigeria
Asali: UGC

A sanarwa ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

Mata Sun Cika Wajen Gangamin Bola Tinubu, Matar Shugaban Kasa ba ta Iya Zuwa ba

“Ba mu da kokwanton cewa gwamnonin Arewa da a baya suka yi alkawarin marawa Tinubu baya za su yi wasa da da wannan alkawarin ba, domin a matsayinsu na musulmi, sun sani sarai cewa kowane alkawari mala’iku ne ke rubuta su kamar yadda Alkur’ani 82 ya fada. (kiraaman kaatibiin); cewa babban zunubi ne ga musulmi ya yi alkawarin abin da ba zai aikata ba, kuma Allah zai yi wa mutum hisabi ga alkawuransa.

“Alhaji Atiku Abubakar Musulmi ne kuma dan Arewa. Saboda haka yana daya daga cikin mu. Amma Ahmed Bola Tinubu da Kashim Shettima Musulmi ne guda biyu. Kamar yadda kawuna biyu suka fi daya, musulmi biyu sun fi daya. Ahmed da Kashim sun fi Abubakar da Okowa".

Al'ummar Musulmi Yarabawa Ta Marawa Tinubu Baya

Al’ummar Musulmin Kudu maso Yammacin Najeriya (MUSWEN) wacce ita ce inuwa daya tilo ta daukacin Musulmi Yarabawa suke kasanta suma su ma sun amince da Tinubu a satin biyun da suka gabata

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Jingine Siyasa, Ya Bayyana Mutumin Da Ya Cancanci Zama Shugaban Kasa a 2023

“Wannan sanarwa na kara nuna cewa KUngiyar MURIC ta Tsaya gam da kafarta bisa goyan bayan wannan takarar haka kuma kungiyar na kira da gwamnonin da suke da shirin ko kokarin yin wannan hali da su hakura su cika alkawari"

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel