Sama da yan Boko Haram 13,000 sun mika wuya, Hedkwatar Tsaron Najeriya

Sama da yan Boko Haram 13,000 sun mika wuya, Hedkwatar Tsaron Najeriya

  • Hukumar Soji ta bayyana adadin yan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya
  • Yan ta'addan sun mika wuya tare da matansu da 'yayansu
  • Onyeuko yace an damke masu kai musu bayanai da kayan abinci.

Abuja - Hedkwatar Tsaro ta bayyana cewa yan ta'addan Boko Haram 13,243 tare da iyalansu suka mika wuya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Mukaddashin Diraktan labarai na hedkwatar tsaro, Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai kan hare-hare da Soji suka kai makonni biyu da suka gabata.

Onyeuko ya zanna da manema labaran a dakin taro dake cikin hedkwatar tsaro ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

A cewar Onyeuko, wadanda suka mika wuya sun hada da maza 3,243, mata 3,868 da yara 6,234.

Ya bayyana cewa jami'an hukumar sun kai hare-hare wurare daban-daban kuma sun samu nasarar kashe yan ta'addan da dama.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021

Onyeuko yace an damke masu kai musu bayanai da kayan abinci.

Sama da yan Boko Haram 13,000 sun mika wuya, Hedkwatar Tsaron Najeriya
Sama da yan Boko Haram 13,000 sun mika wuya, Hedkwatar Tsaron Najeriya Hoto: Dhq
Asali: Facebook

A jawabinsa:

"Mun samu nasarorin ne a Gwoza – Yamtake – Bita road, Gwoza – Farm Centre – Yamtake road, tsaunin Mandara da kuma garin Pulka da Hambagda, duka a Borno."
"A wannan lokaci, an hallaka yan ta'adda 29 kuma mun damke masu kai bayanai da kayayyaki wa yan ta'adda 13."
"Bugu da kari, mun kwace makamai 38, harsasai 968 da kuma dabbobin sata 48 da sauran su."
"Kawo yanzu, jimillar yan ta'adda 13,243 wanda ya hada da maza 3,243, mata 3,868 da yara 6,234 suka mika wuya a Arewa maso gabas."

Babban Hafsan tsaron Najeriya ya tabbatar da kisan Shugaban ISWAP, Mus'ab Albarnawy

Babban Hafsan tsaron Najeriya (CDS), Janar Lucky Irabor, ya tabbatar da kisan shugaban kungiyar yan ta'addan daular Islamiyya a yammacin Afrika ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi.

Kara karanta wannan

An kashe mutane fiye da 1, 300 yayin da Fadar Shugaban kasa ke cewa ana samun tsaro

Janar Irabor ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda hira da manema labarai da fadar shugaban kasa ta shirya a AsoVilla, Abuja, DailyTrust ta ruwaito.

Irabor yace:

"Ina mai tabbatar muku cewa Abu Mus'ab ya mutu. Ya mutu kuma ba ai taba tashi ba."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel