Yadda tsoho mai shekara 72 ya ginawa matarsa abar kaunarsa gida mai jujjuyawa

Yadda tsoho mai shekara 72 ya ginawa matarsa abar kaunarsa gida mai jujjuyawa

  • ani tsoho mai shekaru 72 ya gina wani kalan gida mai jujjuyawa don farantawa matarsa
  • Ya bayyana cewa, matarsa ta jima tana korafi kan yadda tsarin gidansu yake, wannan ne dalili
  • A cikin wata hira, ya bayyana yadda gidan ke iya jujjuyawa cikin sa'o'i 24 kowace rana

Wani mutum ya kai kololuwa wajen farantawa matar sa rai wanda a ko da yaushe take korafin ginin gidansu ta hanyar gina mata gida mai juyawa.

Vojin Kusic mai shekaru 72 daga Bosnia ya zana salon gidan ne daga fikirar masu kirkirar Sabiya-Amurka Nikola Tesla da Mihajlo Pupin.

Yadda tsoho mai shekara 72 ya ginawa matarsa abar kaunarsa gina mai jujjuyawa
Gida mai jujjuyawa | Hoto: reuters.com
Asali: UGC

Gidan na iya juyawa sau daya a cikin awanni 24

A rahoton jaridar Mirror, an ce gidan na iya jujjuyawa a kusa da tsayin mita 7 kuma yana iya tafiya madaidaiciya cikin sa'o'i 24 a cikin hanzari mafi sauri ko cikin dakika 22 cikin sauri.

Kara karanta wannan

Yadda 'Ruwa mai tsarki' ya raba Mata da Miji da suka shekara 10 suna gina soyayya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kusic yayin da ya bayyana a cikin wata hira da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya bayyana, cewa gidan ya dauke shi shekaru 6 kafin ya kammala gina shi, ya bayyana yadda yake da gefe a kan gidajen da ke tsaye.

Ya ce gidan zai iya jure firinar girgizar kasa

Mutumin ya bayyana cewa gidan mai jujjuyawa zai iya jure girgizar kasa, sabanin gine-ginen da ke tsaye.

Yace:

”... Wannan ba kirkira ba ce, kawai tana bukatar niyya da ilimi ne, kuma ina da isasshen lokaci da ilimi.”

'Yan sanda sun cafke 'yan fasa kwabri da mota makare da soyayyun kaji

A wani labarin, 'yan sandan New Zealand sun kama wasu mutane biyu da ke kokarin shigo da mota da ke cike da soyayyun kaji zuwa Auckland, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mun yi amfani da aikin noma wajen tsamo sama da mutum milyan 4 daga Talauci, Ministan Noma

Auckland, birni mafi girma a kasar, yana cikin tsauraran ka'idojin takunkumi na Korona tun tsakiyar watan Agusta, ba tare da an ba kowa izinin shiga ko barin yankin ba.

Duk kasuwancin da ba su da mahimmanci, wanda ya hada da wuraren cin abinci na kan titi, an rufe su a Auckland. Sai dai, sauran yankunan New Zealand na da karancin ka'idoji tare da kusan dukkanin nau'ikan kasuwanci a bude.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.