Me ya yi zafi: Saurayi ya bi buduwarsa har wurin alibidi ya buɗe wa baƙi wuta da bindigarsa
- Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo sun kama wani matashi da ake zargin ya bude wa baki a wani alibidi wuta
- Lamarin ya auku ne a Oba Akoko dake karamar hukumar Akoko ta kudu maso yamma a jihar Ondo
- Kamar yadda bayanai su ka kammala, ya hassala ne lokacin da ya hango budurwar ta sa tare da wani saurayin
Ondo - Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo a ranar Talata ta tabbatar da kama wani mutum wanda ake zargin ya bude wa baki wuta a wani alibidi da aka yi a Oba Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta kudu maso yamma da ke jihar.
Kamar yadda Punch ta ruwaito, a ranar Asabar ana tsaka da shagalin ne wanda ake zargin ya afka wurin ya hau harbe-harbe a cikin bainar jama’a bayan ya hango budurwar sa tare da wani saurayin.
Kallo ya koma sama: Bidiyon ango ɗan Nigeria sanye da siket yana tiƙa rawa a ranar aurensa ya ɗauki hankula
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da dai babu wata asarar rai da aka yi, baki da dama sun samu miyagun raunuka yayin da kowa ya ranta a na kare.
An gano cewa jami’in tsaro ne
Kamar yadda Punch ta ruwaito, wata majiya wacce ta gano wanda ake zargin jami’in tsaro ne ta bayyana yadda saurayin ya bi sawun budurwar bayan ya zarge ta da tarayya da wani saurayin.
Kamar yadda majiyar ta bayyana:
“Wanda ake zargin jami’in tsaro ne duk da dai ba mu tabbatar da wurin aikin sa ba sakamakon yadda yake sanye da kayan gida.
"Ya bi sawun budurwar sa har zuwa wurin alibidin. Ina tunanin harzuka ya yi bayan ya hango ta da wani saurayin ya hau harbe-harbe yana ihu. Harbe-harben ne ya yi sanadiyyar tserewar duk jami’an wurin ciki har da budurwar sa, daga nan aka gama shagalin.”
Wasu mazauna yankin sun ce ya na aiki ne da hukumar bayar da tsaron jihar Ondo, OSSNA, wacce aka fi sani da Amotekun Corps, wasu kuma su ka ce dan sanda ne.
Kwamandan Amotekun ya ce ba jami’in hukumarsa ba ne
Amma kwamandan jami’an tsaron Amotekun, Chief Adetunji ya ce wanda ake zargin ba karkashin hukumar sa yake ba.
Kamar yadda ya shaida:
“Ba mu san komai ba dangane da lamarin kuma babu wani rahoto dangane da hakan da mu ka samu daga yankin Akoko. Wanda ake zargin ba ya cikin mu; kun san mu na da jami’an tsaro da dama, amma ban tabbatar idan cikin mu yake ba.”
Majiya daga ‘yan sanda ta sanar da cewa an mayar da lamarin hedkwatar ‘yan sanda dake Akure don ci gaba da bincike.
Jami’ar hulda da jama’ar ‘yan sandan jihar, Mrs Funnilayo Odunlami ta tabbatar da kama shi, ta kara da cewa yanzu haka ana ci gaba da bincike akan lamarin.
Yayin da ta musanta dan sanda ne wanda ake zargin, ta ki bayar da wani bayani akan sa.
Asali: Legit.ng