A cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote da Bua sun samu karin N30.4b kan dukiyarsu

A cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote da Bua sun samu karin N30.4b kan dukiyarsu

  • Biloniyoyin Najeriya, Aliko Dangote da Rabiu Abdulsamad, su na cigaba da samun shuhura tare da tumbatsar dukiya ta kasuwancin siminti da abinci
  • Arzikin Dangote ya karu da kashi 0.03 yayin da Abdulsamad BUA arzikinsa ya karu da kashi 1.62 wanda ya kai ribarsu N28.85 biliyan da N1.64 biliyan
  • Mamallakin kamfanin siminti na Dangote yanzu haka arzikinsa ya kai $13.4 biliyan, na BUA kuwa ya kai $4.3 biliyan a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba

Aliko Dangote, mamallakin kamfanonin Dangote da Rabiu Abdulsamad, shugaban kamfanin BUA, sun samu ribar tsabar kudi jimilla N30.4 biliyan a cikin sa'o'i 8.

Mashahuran masu arzikin sun samu wannan karin kan dukiyarsu ne a kasuwancin ranar Talata.

Yayin da Dangote har yanzu ya fi kowa arziki a Afrika, mai kamfanin simintin bai kai Abdulsamad Bua samun gagarumar riba ba a ranar Talatan inda dukiyoyinsu suka karu da kashi 0.03 da kuma kashi 1.62 daya bayan daya.

Read also

Kano: Ganduje ya aike da Ƙarin N33.8bn kan kasafin kudin 2021 gaban majalisa

A cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote da Bua sun samu karin N30.4b kan dukiyarsu
A cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote da Bua sun samu karin N30.4b kan dukiyarsu. Hoto daga @habeeb_adamu
Source: Twitter

Arzikin mai kamfanin simintin Dangoten ya karu inda ya kai $13.4 biliyan inda ya cigaba da zama mutum mafi arziki a Najeriya da Afrika.

Kamar yadda kiyasin da ke bibiyar biloniyoyi na Reuters ya bayyana, ya samu karin N1.64 biliyan cikin sa'o'i takwas kacal.

Arzikin Abdulsamad BUA kuwa a daya bangaren ya karu da kashi 1.62 wanda ya kai jimillar dukiyarsa zuwa $4.3 biliyan bayan ya samu karin zunzurutun kudi har N28.85 cikin sa'o'i takwas kamar yadda kiyasin biloniyoyi ya bayyana.

A yayin da dukiyarsa ta kai $13.4 biliyan a ranar Talata, Dagote ya zama mutum na 191 a jerin biloniyoyin duniya, yayin da Abdulsamad ya hau mataki na 574.

Mu sani cewa, Dangote da Abdulsamad suna gasa a masana'antu iri daya inda suke sarrafa siminti, sikari da gishiri. Biloniyoyin 2 a halin yanzu su na hangen masana'antar man fetur ne.

Read also

Gwamna El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2022 ga majalisar dokokin Kaduna

Kano: Ganduje ya aike da Ƙarin N33.8bn kan kasafin kudin 2021 gaban majalisa

A wani labari na daban, Gwamnan Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya aike da karin kasafin kudi har N33.8 biliyan gaban majalisar jihar domin ta amince da shi. Kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya karanta wannan bukatar a zauren majalisar jihar Kano a ranar Talata.

Kamar yadda bukatar gwamnan ta bayyana, N3.22 biliyan zai biyan ma'aikata yayin da N9.2 za a kashe su kan bukatun yau da kullum, sai kuma N21.5 biliyan ta manyan ayyuka, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, da karin kasafin N33 biliyan, jimillar kasafin kudin shekarar 2021 za ta tsaya a N231.7 biliyan.

Source: Legit

Online view pixel