Dole PDP ta mika shugabancin kasa na 2023 ga yankin Kudu maso gabas, in ji Ikpeazu

Dole PDP ta mika shugabancin kasa na 2023 ga yankin Kudu maso gabas, in ji Ikpeazu

  • An bukaci jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ta mika tikitin takarar shugaban kasa na 2023 zuwa kudu maso gabas
  • Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ne ya yi wannan kiran a gidan gwamna a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba
  • Ikpeazu ya ce zai zama adalci ne kawai idan jamiyyar ta tabbatar ganin dan takarar shugaban kasa na 2023 na PDP ya fito daga yankin

Abia - Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, ya ce yana da muhimmanci ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta mika tikitinta na takarar shugaban kasa na 2023 zuwa yankin kudu maso gabashin kasar.

PM News ta ruwaito cewa gwamnan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Abia, ya ce kudu maso gabas bata samar da shugaban kasa ba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Jerin manyan jiga-jigan PDP da ke son a bude tikitin jam’iyyar ga dukkan yankuna

Dole PDP ta mika shugabancin kasa na 2023 ga yankin Kudu maso gabas, in ji Ikpeazu
Dole PDP ta mika shugabancin kasa na 2023 ga yankin Kudu maso gabas, in ji Ikpeazu Hoto: Okezie Ikpeazu
Asali: Facebook

Mayar da yankin kudu maso gabas saniyar ware

Ya ce ya kamata a mikawa kudu maso gabas tikitin takarar shugaban kasa na 2023 ba tare da bata lokaci ba saboda an dade ana mayar da yankin saniyar ware.

Gaskiya, daidaito da adalci ga mutanen kudu maso gabas

A cewar gwamnan, ya kamata a bai wa yankin tikitin takarar shugaban kasa na PDP a shekarar 2023 a cikin gaskiya da adalci, Daily Post ta kuma rahoto.

Ikpeazu ya ce:

"Kamar yadda PDP ta karkatar da shugabancin ta zuwa arewa, yakamata kujerar shugaban kasa ta koma kudu maso gabas.
"PDP ce ta fitar da zabinmu na yanki kuma ta ce ya kamata shugaban jam'iyyar ya koma Arewa a 2023."

Kara karanta wannan

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

2023: Ina gabatar da Atiku ga 'yan Najeriya, babu dan takarar kudu da zai iya lashe zabe – Jigon PDP

A wani labarin, Cif Raymond Dokpesi, jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya ce babu dan takarar kudu da zai iya lashe wa jam’iyyarsa zaben shugaban kasa na 2023.

Dokpesi ya yi wannan ikirarin ne a cikin wata hira da jaridar Daily Trust ta buga a ranar Asabar, 9 ga Oktoba.

Koda yake yace babu wani dan takara daga kudu maso gabas da zai iya yin nasara a 2023, Dokpesi ya ce yankin ya cancanci samun kujerar idan aka mika kujerar shugabanci zuwa yankin kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng