An ce ba zan taba aure ba, amma Allah ya kunyatasu: 'Yar shekara 64 da tayi aurenta na farko

An ce ba zan taba aure ba, amma Allah ya kunyatasu: 'Yar shekara 64 da tayi aurenta na farko

  • Yar shekara 64, Erumena Amata, ta yi aurenta na farko a rayuwarta duk da maganganun mutane
  • Matar ta bayyana cewa har 'yayan da aka haifa gabanta sun yi aure sun hayayyafa
  • Erumena Amata, tace gidan miji ne abu daya da ta dade tana son zama

Bayelsa - Wata 'yar Najeriya mai suna Erumena Amata, wacce mutane suka dade suna fada mata ba zata taba aure ba ta samu masoyinta bayan gomman shekaru.

A hirar da tayi da BBC News Pidgin, matar tace mutane sun dade suna fada mata ta girma da yawa ba zata samu mijin aure ba.

Ko da namiji yazo sai in ga bai min ba

Tace ko da maza sun zo nemanta, za ta ga basu mata ba, imma ta ga gajere ne ko kuma ta girmesa sosai.

Read also

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A cewarta, Allah ya kunyata masu yi mata isgili.

Tace kowace shekara ta kanyi addu'a Allah yasa tayi Kirismeti mai zuwa a gidan mijinta,

Tace ko yaran da aka haifa gabanta sun yi aure kuma sun haifi nasu yaran.

An ce ba zan taba aure ba, amma Allah ya kunyatasu: 'Yar shekara 64
An ce ba zan taba aure ba, amma Allah ya kunyatasu: 'Yar shekara 64 da tayi aurenta na farko Photo source: @bbcnewspidgin
Source: Instagram

Abinda ya ja min rashin samun miji

Erumena tace irin rayuwar da tayi a baya na kokarin zaben mutumin da bai da aibi ko guda ya haddasa mata rashin miji.

Tace sabon mijinta ya aure ta ne bayan shekaru 10 da mutuwar matarsa.

Ga bidiyon hirar:

Source: Legit

Online view pixel