Alaka da yan bindiga: Majalisar dokokin Zamfara ta dakatad da mambobinta biyu

Alaka da yan bindiga: Majalisar dokokin Zamfara ta dakatad da mambobinta biyu

  • Ana zargin yan majalisu biyu a Zamfara da alaka da tsagerun yan bindiga
  • An dakatad da yan majalisun na tsawon watanni uku don bincike
  • An tuhumi yan majalisan da hannu cikin kisan wani abokinsu dan majalisa

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatad da mambobinta biyu, kan zargin da ake musu cewa suna da alaka da yan bindiga masu garkuwa da mutanen da suka addabi jihar.

Yan majalisar da aka dakatar sune Yusuf Muhammad mai wakiltan Anka da kuma Ibrahim Tukur mai wakiltan mazabar Bakura, rahoton DailyTrust.

An dakatad da su ne na tsawon watanni uku.

A sanarwar da Diraktan yada labaran majalisar, Mustapha Jafaru Kaura, ya saki, an umurci yan majalisan su nisanta kansu daga majalisar har sai an kammala binciken da ake gudanarwa kansu.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya kafa majalisar tantance wa'azi da Malamai masu wa'azi a jihar Kaduna

Yace:

"Zasu bayyana gaban kwamitin ladabi tare da hadin gwiwan jami'an tsaro da zasu yi bincike kansu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan na cikin abubuwan da akayi ittifaki kai a zaman majalisan da Kakaki Rt Hon Nasiru Mu’azu Magarya ya jagoranta."

Alaka da yan bindiga: Majalisar dokokin Zamfara ta dakatad da mambobinta biyu
Alaka da yan bindiga: Majalisar dokokin Zamfara ta dakatad da mambobinta biyu
Asali: UGC

Me yasa aka dakatad da su

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Maru ta Arewa, Hon Yusuf Alhassan Kanoma, ya bayyana cewa ba zasu zuba ido kan zarge-zargen da ake wa yan majalisun biyu ba.

Yace lokacin da aka sace mahaifin Kakakin Majalisar Alhaji Mu’azu Abubakar Magarya, sun samu labarin yan majalisun biyu Yusuf Muhammad Anka da Ibrahim T Tukur Bakura murna sukeyi.

Ya kara zarginsu da hannu wajen kisan Hanarabul Muhammad G Ahmad (Walin Jangeru), wani tsohon dan majalisan da ya wakilci Shinkafi.

Ya yi kira ga jami'an tsaro su binciki wayoyin yan majalisun biyu.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya ware Naira miliyan miliyoyi, zai biya kudin karatun yara 600 a garuruwan Legas

A karshen zaman, Kakakin majalisar ya amince da a dakatad da su kuma a kaddamar da bincike kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel