Da duminsa: Wasu yan bindiga sun budewa gwamnan Anambra wuta
- Yna bindiga sun kaiwa gwamnan jihar Anambra da tawagarsa hari
- An kwashe sama da awa guda ana artabu tsakaninsu da jami'an tsaro
- Akalla mutum shida sun rasa rayukansu a wannan mumunan hari
Anambra - Wasu yan bindiga dadi sun kaiwa Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, wuta ranar Talata a wajen taron yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, Jaridar DailyTrust ta ruwaito.
Wannan abu ya auku ne a makarantar Sakandaren dake Ihiala inda aka kwashe sama da sa'a daya ana musayar wuta tsakanin yan bindiga da masu tsaron gwamnan.
A cewar rahoton, an kashe jami'in Soja guda daya kuma akalla mutane shida sun mutu yayinda da dama sun jikkata.
A wata riwayar, gwamnan ya gaza fita daga wajen na sama da awa guda sakamakon harbe-harben.
Wata majiya tace:
"Motocin gwamnan sun gaza wucewa na kimanin awa guda, saboda harbe-harbe kawai akeyi."
Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da aukuwan wannan abu ya ce jami'an yan sanda sun kawar da yan bindigan a Odata.
A cewarsa, an kwato bindgar AK47 guda, gidan harashi 2 mai dauke da harsasai 30, lexus 350 jeep 1, Rav 4 jeep 1, Mercedes Benz 1 da Toyota Corolla.
Tsokacin Kwamishanan labaran jihar Anambra
Tsokaci kan lamarin, kwamishanan labaran jihar, Mr. C.Don Adunuba, ya ce gamayyar yan sanda da Sojoji sun kawar da harin.
Yace yan bindiga sun sha wutar annaru wajen jami'an tsaro har suka gudu cikin wani asibitin Our Lady of Lourdes dake gaban filin kamfen.
Yace:
"Da yan bindiga basu gudu cikin asibitin ba wanda waje ne mai hadari da ba za'a bisu ba, da jami'an tsaro sun kashesu duka."
Jawabin Gwamnan bayan harin
Gwamnan jihar bayan tsira daga harin ya jinjinawa Sojoji da yan sandan da suka kawar da yan bindigan.
Yayin jawabi ga manema labari a Atani, yace jami'an tsaron sun yi abin a zo a gani.
Asali: Legit.ng