Dan Najeriya ya yi wuf da tsaleliyar matarsa 'yar Amurka bayan ta yi masa tayin soyayyar ta

Dan Najeriya ya yi wuf da tsaleliyar matarsa 'yar Amurka bayan ta yi masa tayin soyayyar ta

  • Wani dan Najeriya ya bayyana yadda rayuwar su ta kasance da baturiyar matar sa
  • Kamar yadda ya ce, baturiyar da kan ta ta yi ma sa tayin soyayyar ta ta Facebook
  • Ya wallafa hotunan su tare da zankadediyar matar ta sa cike da shaukin soyayya

Wani dan Najeriya ya wallafa yadda rayuwar sa da zukekiyar matarsa 'yar Amuka ta kasance bayan ya aure ta kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kamar yadda ya wallafa hotunan su har da hirar su ta farko da su ka yi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wanda ya yi wa take da 'Yadda aka fara da yadda ake ci gaba da rayuwa'.

Dan Najeriya ya yi wuf da tsaleliyar baturiya bayan ta yi masa tayin soyyar ta
Dan Najeriya ya yi wuf da tsaleliyar baturiya bayan ta yi masa tayin soyyar ta
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kallo ya koma sama: Bidiyon ango ɗan Nigeria sanye da siket yana tiƙa rawa a ranar aurensa ya ɗauki hankula

Cike da soyayya, ya wallafa wasu zafafan hotunan da su ka dauka tare, kuma alamu su na nuna su na matukar kaunar juna.

Da farko ya fara wallafa hotunan hirar sa da matar inda ya nuna yadda ta fara tura ma sa hoton ‘yan aljanun nan na hirar kafafen sada zumunta ma su dauke da alamar soyayya.

Dan Najeriya ya yi wuf da tsaleliyar baturiya bayan ta yi masa tayin soyyar ta
Dan Najeriya ya yi wuf da tsaleliyar baturiya bayan ta yi masa tayin soyyar ta. Hoto: Shanice Enenche Weber
Asali: Instagram

Dan Najeriya ya yi wuf da tsaleliyar baturiya bayan ta yi masa tayin soyyar ta
Dan Najeriya ya yi wuf da zukekiyar baturiya bayan ta yi masa tayin soyyar ta. Hoto: Shanice Enenche Weber
Asali: Instagram

Baturiyar ta yaba da kyawun sa

Ta fara da ce ma sa kyakkyawa kuma ta bukaci sanin idan shi dan nahiyar Afirka ne.

Ya sanar da ita cewa shi cikakken dan Najeriya ne daga nan ta ke sanar da shi ita baturiya ce ‘yar Amurka.

Ta nuna ma sa farin cikin ta kwarai da ta samu damar zantawa da shi cikin ladabi.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, hirar ta su ta ci gaba kwarai dagan nan su ka fara soyayyar ta kai su ga aure.

Kara karanta wannan

Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji

Matashin ya nuna yadda cike da girmamawa da mutumtaka baturiyar ta gabatar ma sa da ra’ayin ta na soyayya da shi.

Daga wallafar ta sa za ka gane yadda yake madalla da auren baturiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel