Jerin wasu nasarori 12 da Buhari ya cimma a shekaru 2, wa'adin mulkinsa na biyu

Jerin wasu nasarori 12 da Buhari ya cimma a shekaru 2, wa'adin mulkinsa na biyu

 • A wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, tuni ya ci shekaru biyu a ciki yanzu
 • A wani taro, shugaban ya lissafo wasu nasarori da gwamnatinsa ta cimma cikin shekaru biyu
 • Daga rahotanni masu tushe, mun tattaro muku jerin wasu daga cikin nasarorin da ashugaban ya cimma

Abuja - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Shekaru biyu cikin wa'adin mulkinsa na biyu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba ya lissafa nasarorin da ya cimma a Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake magana a wani taron ganawa da ministoci don tantance ayyukan gwamnatin sa.

Taron ganawar ya baiwa ministoci da shugabannin hukumomin dama su baje kolin ayyukansu don tantancewa tare da nuna ko sun dace da manufofin gwamnatin gaba daya.

Read also

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

Jerin wasu nasarori 12 Buhari ya cimma a shekaru 2, wa'adin mulkinsa na biyu
Shugaba Buhari ya bayyana irin nasarorin da ya cimma a wa'adin mulkinsa na biyu | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Ga wasu daga cikin nasarori da shugaba Buhari ya lissafo

 1. Gadar Neja ta Biyu mai tsawon kilomita 11.9
 2. Babbar hanyar Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 120
 3. Babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano mai tsawon kilomita 375
 4. Hanyar Gabas ta Yamma
 5. Kafa kamfanin InfraCo Plc a shekarar 2020
 6. Kaddamar da Asusun kirkira na Najeriya da Hukumar Zuba Jari ta Najeriya (NSIA)
 7. Titin jirgin kasa na Itakpe zuwa Ajaokuta
 8. Aiwatar da Manufofin ‘Mai Saye-da-Sayarwa’
 9. Sa hannu kan dokar Masana'antar Man Fetur a cikin doka a ranar 16 ga Agusta
 10. Karfafawa matasa da sauran kungiyoyi masu rauni
 11. Shirin Ba da Kudi duba da Yanayi
 12. Kafa Asusun Zuba Jari na Matasan Najeriya na Naira Biliyan 75

Bayan korar ministoci biyu, Buhari ya gargadi ministocinsa kan aiki tukuru

Read also

Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama

A wani bangaren taron, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba ya karanto dokar tarzoma ga ministoci a majalisar ministocinsa da sakatarorin dindindin a fadin ma'aikatu.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa shugaban ya bukaci jami'an da su dauki batutuwan aiwatar da ayyukan da aka dora masu da muhimmanci.

Shugaban ya ce yana da mahimmanci jami'an su sani cewa sauke nauyin ayyukansu da muhimmanci zai taimaka wa gwamnatin yanzu ta cimma burin ta da alkawuran da ta yiwa 'yan Najeriya.

Source: Legit

Online view pixel