Malaman Kano sun yi martani kan cewa sun tsige shugaban malamai Sheikh Khalil

Malaman Kano sun yi martani kan cewa sun tsige shugaban malamai Sheikh Khalil

  • Hadin gwiwar malamai a jihar Kano sun yi watsi da batun dakatar da Sheikh Ibrahim Khalil
  • A cewarsu, ba da yawunsu aka dakatar da malamin ba, kuma basu ma san da hakan ba kwata-kwata
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da aka yada rahoton malaman Kano sun dakatar da Sheikh Khalil

Kano - Gamayyar malamai da kungiyoyin addinin muslunci a jihar Kano, sun yi watsi da sanarwar da ke cewa an tsige shugaban majalisar malamai ta jihar Kano.

Rahotanni da dama sun yadu a kafafen sadarwa, inda aka bayyana majalisar ta tsige Sheikh Ibrahim Khalil a matsayin shugaban majalisar malamai na jihar Kano.

A cikin wata sanarwar da ta shigo hannun Legit.ng Hausa, kungiyar malaman ta Kano sun yi watsi da batun, inda suka ce ba da yawunsu hakan ta faru ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Za'a daina bada tazara a sahun Sallah daga gobe Lahadi a Makkah da Madina

Malaman Kano sun yi martani kan tsige Sheikh Kalil
Sanarwar da malamai suka fitar | Hoto: freedomradionig.com
Asali: UGC

Sanarwar mai dauke da sa hannun Dr Saidu Ahmad Dukawa an fitar da ita ne a yau Talata, 12 ga watan Oktoba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jerin malamai 8 da sunayensu ya fito a cikin sanarwar watsi da tsige Sheikh Ibrahim Khalil

Legit.ng Hausa ta lura cewa, sanarwar na dauke da sunayen wasu manya kuma jiga-jigai a kungiyar ta hadin kan malamai wadanda suka hada da:

  1. Farfesa Musa Muhammad Borodo
  2. Khalifa Sheik Karibullah Sheik Nasiru Kabara
  3. Sheikh Abdulwahab Abdallah
  4. Sheikh Ibrahim Shehu Maihula
  5. Farfesa Muhammad Babangida Muhammad
  6. Dr Bashir Aliyu Umar
  7. Imam Nasir Muhammad Adam
  8. Dr Ibrahim Mu'azzam Mabushira

Majalisar Malaman Kano ta dakatar da Sheikh Khalil daga shugabanci saboda abu biyu

A wani labarin, Majalisar malamai ta jihar Kano, ta dakatar da shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Majalisar ta bayyana dakatar da babban malamin ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a jihar Kano.

Legit.ng Hausa ta gano cewa tuni majalisar ta maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, a matsayin shugaban rikon kwarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.