Hadimin Buhari ya bayyana abin da zai faru da masu neman hada Tinubu fada da Osinbajo
- Babafemi Ojudu yace sun san da zaman masu neman raba kan shugabannin APC
- Sanata Ojudu yake cewa wasu na son hada Bola Tinubu da Yemi Osinbajo rigima
- Hadimin Shugaban kasar ya gargadi magoya baya kan fara yakin 2023 tun yanzu
Abuja - Mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu, ya yi magana game da abubuwan da ke faru wa a siyasar gidan APC.
Punch tace Sanata Babafemi Ojudu ya yi tsokaci kan masu neman jawo rigima tsakanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Bola Tinubu.
Da aka yi hira da hadimin shugaban kasar a gidan talabijin na Channels TV a shirin Sunrise Daily, yace ana ta kokarin gwara kan ‘yan siyasar a zaben 2023.
Wadanda aka yi hira da su a shirin sun hada da Alwan Hassan, wanda gawurtaccen masoyin Osinbajo da wani ‘dan tafiyar Bola Tinubu, Tunde Ajibulu.
Sanata Ojudu yake cewa da uban gidansa, mataimakin shugaban kasa Osinbajo da jagoran APC, Bola Tinubu, duk ‘ya ‘yan APC ne da babu gaba a tsakaninsu.
A cewar Ojudu, babu wani sabani ko rikici a halin yanzu da ya shiga tsakanin ‘yan siyasar biyu. Sannan yace ba a bada dama a fara buga gangunan siyasa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar tace Ojudu ya fitar da jawabi na musamman, yana cewa duk mai yunkurin ganin Yemi Osinbajo ya yi fada da tsohon gwamna, Tinubu, zai ji kunya.
Daily Trust tace an yi wa jawabin take da 2023 Presidential Election: No To Divisive Politics, Attempts To Foist A Crack Between Osinbajo, Tinubu Will Fail’.
Jawabin da Sanata Babafemi Ojudu ya fitar
“Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ‘yan jam’iyya guda ne.”
“Don haka Osinbajo yana daukar Tinubu a matsayin jagorar tafiyar siyasar da yake ciki, a dalilin wannan ba zai goyi bayan abin da zai hada su rigima ba.”
“Muna sane da masu kokarin kawo sabani tsakanin shugabanninmu. Yunkurin ba zai je ko ina ba. Alakar Osinbajo da Tinubu ta tare, sai kara danko take yi.” - Ojudu
Tsohon Sanatan ya yi kira ga ‘yan jarida da daidaiku su guji jawo sabani, yace a kyale APC ta cigaba da zama a dunkule, yace Osinbajo ya na biyayya ga jagororinsa.
A karshe Ojudu ya yi wa Tinubu maraba da dawo wa Najeriya, ya yi kira ga wadanda suka fara zuga ‘yan siyasar su nemi takara a 2023, su dakata har sai lokaci ya yi.
Ra'ayin Sanata Ronaldo Ovie a kan 2023
An rahoto Ronaldo Ovie yana cewa adalci shi ne PDP ta ba ‘Dan Arewa takarar Shugaban kasa a 2023 domin 'Yan kudu sun yi shekara 14 suna mulki tsakanin 1999-2015.
Sanata Ronaldo Ovie yace bai kamata wani ya hana PDP tsaida ‘Dan Arewa a takarar Shugaban kasa ba
Asali: Legit.ng