‘Dan siyasar Kudu yana kira ga PDP ta ba Arewa damar takarar 2023, ya kawo hujja mai karfi

‘Dan siyasar Kudu yana kira ga PDP ta ba Arewa damar takarar 2023, ya kawo hujja mai karfi

  • Sir Roland Owie yana ganin ‘Dan Arewa ya dace da tutar PDP a zabe mai zuwa
  • Sanatan ya yi kira ga Jam’iyyar PDP ta kai tikiti zuwa yankin Arewacin Najeriya
  • Owie yace daga 1999, ‘Yan Kudu sun samu mulki na shekaru 14 a Jam’iyyar PDP

Benin - Tsohon mai tsawatar wa a majalisar dattawa, Sir Roland Owie, ya yi kira ga shugabannin PDP su kai takarar shugaban kasa zuwa yankin Arewa.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021, inda aka ji Sanata Roland Owie yana goyon bayan Arewa ya samu mulki.

Da yake hira da ‘yan jarida a garin Benin, jihar Edo, Roland Owie yace adalci da zaman lafiya shi ne PDP ta ba ‘dan Arewa tikitin neman shugaban kasa.

Read also

Kungiyar Arewa ta bada shawarar yadda za a shawo kan matsalolin da ake fama da su

Abin da Sanata Owie ya dogara da shi, shi ne shekaru uku kacal ‘yan Arewa suka yi rike da shugaban Najeriya tun 1999 a karkashin jam’iyyar PDP.

Hujjar da Sir Owei ya kafa

“PDP ce kadai jam’iyyar da ta yarda da hadin-kan kasar nan. Shugabancin kasa ya koma Arewa. Ka da wani ya hana PDP yin abin da ya kamata.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Tun shekarar 1999, ‘Yan siyasar Kudu ta hannun Cif Olusegun Obasanjo da Dr. Goodluck Jonathan, sun yi tsawon shekaru 14 a kan mulkin kasar."
“Arewa a karkashin marigayi Umaru Musa Yar’Adua, sun yi mulki na kasa da shekaru uku.” - Owie

‘Dan siyasar Edo
Sir Roland Owie Hoto: forefrontng.com
Source: UGC

Owie ya bada misali da karar da Arewa ta yi wa Obasanjo

Rahoton yace Sanata Owie ya dauko tarihi, yace Obansajo ya zama shugaban kasa a 1999 ne saboda rashin adalcin da aka yi wa yankinsa a zaben 1993.

Read also

Watanni 4 da sauya-shekar gwamna zuwa APC, PDP tace ana neman rusa mata hedikwata

Owie yace Obasanjo ya yi mulki na shekaru takwas duk da ya sha kashi har a rumfar zabensa. Daga nan mulki ya koma Arewa, sai ya sake koma wa Kudu.

Roland Owie ya fada wa manema labarai cewa idan ba don tsarin karba-karba ba, zai yi wahala ‘Yan Kudu su amu mulki, domin kuri’u sun fi yawa a Arewa.

Sir Roland Owie mai shekara 76 ya taba wakiltar Edo ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya.

A jiya kun ji cewa 'yan siyasa irinsu Bode George suna da akasin wannan ra'ayi, yana ganin idan an ba ‘Yan Arewa shugaban jam’iyya, sai a kai takara Kudu.

Cif Bode George wanda jigo na a PDP yace tun 1999 haka abin yake, ya fadi dalilin da ya sa za a ba 'Yan Kudu damar tsaya wa neman takarar shugabancin kasa.

Source: Legit

Online view pixel