Dan fansho ya yanke jiki ya faɗi yayin da suke zanga-zangar neman a biya su hakkinsu

Dan fansho ya yanke jiki ya faɗi yayin da suke zanga-zangar neman a biya su hakkinsu

  • Wani dan fansho ya yanke jiki ya fadi a kan titin Ring Road dake Benin, jihar Edo
  • Su na tsaka da zanga-zanga akan rashin biyan su hakkin su kudin sallama ne lamarin ya faru
  • Take anan ‘yan kungiyar ta su suka yi gaggawar wucewa da shi asibiti don samun kulawa

Jihar Edo - Wani dan fansho ya yanke jiki ya fadi a kan titin Ring road da ke Benin, jihar Edo yayin da mambobin kungiyar samar da walwalar ma’aikatan gwamnatin Najeriya, ARCSWON, su na tsaka da zanga-zanga a ranar Litinin.

‘Yan fanshon su na zanga-zanga ne bisa rashin biyan su kudaden fansho da kudin sallama da sauran kudaden walwalar su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dan fansho ya yanke jiki ya faɗi yayin da suke zanga-zangar neman a biya su hakkinsu
Masu zanga-zangar fansho a Edo. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Read also

Pandora Papers: An sake bankaɗo manyan kamfanonin gwamnan APC na 3 na ƙasar waje

Take anan ‘yan kungiyar su ka yi gaggawar wucewa da shi asibiti don samun taimakon gaggawa.

‘Yan fansho rike da takardu wadanda aka yi rubutu kamar 'Yan fansho su na bukatar kudaden sallama don kulawa da lafiyar mu', 'A biya mu kudaden sallama don mu hada da fanshon watan mu,' da sauran su.

Take anan titin ya cakwude

Zanga-zangar ta janyo cakudewar titin da sauran titina wanda sakamakon hakan masu ababen hawa su ka dinga sauka su na takawa a kasa.

Daily Trust ta ruwaito yadda Kakakin kungiyar, Yusuf Bako, ya ce su na yin zanga-zangar ne sakamakon cire mu su kudade da ake yi daga cikin kudin fanshon su da sauran su.

Kamar yadda ya bayyana:

“A batun kudin sallama, tun 2012, gwamnati ba ta saka masu murabus da ga ayyuka kudin sallamar su ba, sannan kananun hukumomi kuma tun 2008 ne.”
“Mu na da matsaloli akan fanshon mu, a matsayina na malami wanda ya karantar da Geography, N4,000 ake ba ni duk wata.”

Read also

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A cewar sa wannan zanga-zangar ta jan kunnen gwamnatin jihar ne don gagarumar ta na nan zuwa idan ba ayi gyara akai ba.

Bako ya kara da cewa:

“A ranar, za mu dauki tukwane, gado da murhu mu cike wurinnan komai ruwa komai rana, ba za mu bar titin nan ba har sai sun biya mana bukatun mu. Amma yau za mu dakata saboda an fara tattaunawa akan matsalolin mu.”

Yayin tattaunawa da ‘yan fanshon, Osaro Washington, wakilin hukumar fansho ta jihar Edo, ya tabbatar mu su da cewa za a yi kokarin kawo gyara da tallafi gare su.

Kamar yadda ya ce:

“Mun bukaci a dakata da cire 1% daga cikin kudin fansho. Babu wani dan fansho da yake bin mu ko sisi. Su na korafi ne akan kudin sallama.”
“Mun sanar da su da dadewa cewa za mu yi gaggawar biyan su kuma yanzu haka mu na ta taro ne da masu ruwa da tsaki akan lamarin.”

Read also

Ku yi magudi a zaben Anambra, ku mutu a hatsarin jirgin sama – Fasto ta gargadi ‘yan siyasa

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Source: Legit

Online view pixel