Wata sabuwa: 'Yan awaren IPOB sun haramta cin 'Naman Shanun Fulani' a kudu maso gabas

Wata sabuwa: 'Yan awaren IPOB sun haramta cin 'Naman Shanun Fulani' a kudu maso gabas

  • Kungiyar 'yan awaren IPOB sun haramta cin naman shanun Fulani a yankin kudu maso gabas na kasar nan
  • Kamar yadda daraktan kungiyar, Chika Edoziem ya sanar, dokar za ta fara aiki ne a watan Afirilun shekara mai zuwa
  • Daga kan birniya, bikin aure, bikin sarauta, an hana kai shanun Fulani idan ba wadanda aka kiwata a yankin ba

Kudu maso gabas - Kungiyar masu son kafa kasar Biafra ta IPOB, ta haramta cin naman shanu a yankin kudu maso gabas, TheCable ta wallafa.

A wata takarda da aka fitar a ranar Asabar ta hannun Chika Edoziem, daraktan kungiyar, ya ce kungiyarsu ta ce wannan haramcin zai fara aiki a watan Afirilun 2022.

Wata sabuwa: 'Yan awaren IPOB sun haramta cin 'Naman Shanun Fulani' a kudu maso gabas
Wata sabuwa: 'Yan awaren IPOB sun haramta cin 'Naman Shanun Fulani' a kudu maso gabas. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

Kungiyar IPOB, wadanda suka dinga saka dokar zaman gida dole a yankin kudu maso gabas, ta ce wannan haramcin zai kawo karshen matsanancin harin da ake kai wa jama'a a yankin kudu maso gabas.

Read also

Kasafin kudin 2022: Fadar shugaban kasa za ta kashe N1.6bn wurin siyan sabbin ababen hawa

Tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ranar 8 ga watan Afirilun 2022 ita ce ranar, daga ranar, ba bu shanun Fulani da za a sake bari su shigo kasar Biafra, ko saboda birniya, sarauta, bukukuwa da sauransu," takardar tace.
Edoziem ya kara da cewa, "Shanun da aka kiwata a yankinmu kadai za mu bari ana ci tare da amfani da su wurin shagulgula a kasar Biafra".

A watan Fabrairu, IPOB ta yi barazanar tabbatar da dokar hana kiwo a yankin, TheCable ta wallafa.

Kungiyar ta ce duk wadanda suka taka dokar za su "fuskanci irin haukar da ba su taba gani ba".

Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3

A wani labari na daban, dakarun sashi na 5 na atisayen Golden Dawn da aka tura Enugu sun sheke mutum 3 da ake zargin 'yan awaren kudu ne da aka fi sani da IPOB, wadanda suka kai wa 'yan sanda farmaki kan babbar hanyar Okija zuwa Onitsha a ranar 7 ga watan Oktoba.

Read also

Terere: Yadda Fasto Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kamar yadda takardar da kakakin dakarun sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar tace, zakakuran sojin sun yi artabu da miyagun kuma suka fi karfinsu, lamarin da yasa suka arce.

"Dakarun sojin ba su kakkauta ba suka bi su tare da cigaba da zuba musu ruwan wuta. Uku daga cikin 'yan bindigan da ke tuka motoci biyu kirar Hilux da Hummer bus ne suka bakunci lahira yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika."

Source: Legit

Online view pixel