Kasafin kudin 2022: Fadar shugaban kasa za ta kashe N1.6bn wurin siyan sabbin ababen hawa

Kasafin kudin 2022: Fadar shugaban kasa za ta kashe N1.6bn wurin siyan sabbin ababen hawa

  • Kasafin kudin shekarar 2022 ya bukaci a cire kudi har N1.6 biliyan domin siyan sabbin ababen hawa
  • Ministan kudi, Zainab Shamsuna Ahmed ta ce duk da halin rashin kudin da kasar ke ciki, za a aro domin aiwatar da ayyukan
  • Sanata Ali Ndume na jihar Borno ya nuna damuwarsa inda ya ce zai fi kyau a zabtare kudaden amfanin 'yan siyasa a kan aro

Fadar shugaban na son a ware mata sununun dukiya har N1.6 biliyan domin siyan sabbin ababen hawa da bangarorinsu, Daily Trust ta wallafa.

Wannan ya na kunshe ne a kasafin kudin shekara mai zuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika gaban majalisar wakilai da ta dattawa a ranar Alhamis.

Kasafin kudin 2022: Fadar shugaban kasa za ta kashe N1.6bn wurin siyan sabbin ababen hawa
Kasafin kudin 2022: Fadar shugaban kasa za ta kashe N1.6bn wurin siyan sabbin ababen hawa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ministan kudi, Zainab Ahmed, ta ce gwamnatin za ta san hanyoyin samo wadannan kudaden da aka kasafta ko ta hanyar sake aro kudade ne, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista

Kamar yadda kiyasin ya bayyana, sauya ababen hawan da bangarorinsu za su kwashe N1.6 biliyan idan aka alakanta shi da N436 miliyan na shekarar da ta gabata da aka cire.

A kalla N180,089,000 aka ware domin siyan tayoyin ababen hawa da harsashi ba su hudawa, motoci, ababen hawan CCU, manyan motocin daukan kaya, jifa-jifai, motocin asibiti da sauransu.

A shekarar da ta gabata, an ware N116,194,297 domin irin wannan bukatar.

Sanata Ali Ndume na jihar Borno daga jam'iyyar APC ya kwatanta lamarin da abun tashin hankali, kan yadda gwamnatin ke son aro kudi domin aiwatar da ayyukan da kasafin kudin ke kunshe.

A maimakon hakan, ya shawarci mahukuntan da su zabtare duk wani kudi da aka ware domin amfanin kan su da kuma ayyukan yau da kullum tare da kara kudin shiga da kuma toshe duk wani wuri da ke lashe kudi.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 10 da Shugaba Buhari ya fada a jawabinsa ga yan majalisa ranar Alhamis

A kasafin kudin 2022, Buhari ya bukaci N5.23bn na gyaran fadar shugaban kasa

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa na bukatar kudi har N5.231,101,743 domin gyaran fadar shugaban kasa tare da gyaran wasu kadarorin da ke ciki a kasafin kudin shekarar 2022 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika gaban majalisar dattawa.

A duban da aka yi wa kasafin kudin, an gano cewa gyaran gine-ginen ofisoshi zai lamushe N5,176,045,297, yayin da ginen gidajen ciki zai kwashe N55,056,446 daga cikin N150,590,609,934 wanda fadar shugaban kasan za ta kashe, Daily Trust ta ruwaito.

A kasafin kudin shekarar 2021, an ware N4,854,381,299 na gyaran injina da kuma kayan wuta a cikin fadar shugaban kasan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel