Atiku da Saraki na kitsa kwace PDP daga gwamnoninta, su sake dawo da Secondus

Atiku da Saraki na kitsa kwace PDP daga gwamnoninta, su sake dawo da Secondus

  • Jam'iyyar PDP ta mika babban mukamin jam'iyyar zuwa Arewa a wani taron da ya gabata
  • A halin yanzu, yankin na Arewa bai bayyana takamaimai wanda za a ba wannan mukami ba
  • Rahoto ya bayyana cewa, akwai yiyuwar mika mukamin ga daya daga cikin wasu jiga-jigan jam'iyyar a Arewa

Rahoton da jaridar ThisDay ta fitar ya nuna cewa shugabannin Arewa na tunanin yin amfani da zabin da aka amince da shi na zaben shugaban jam'iyyar PDP, bayan karkatar da ofishin ga yankin.

Rahoton, duk da haka, ya nuna cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark da tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido sune na gaba-gaba a takarar neman mukamin.

Sai dai, masoya ga Atiku Abubakar da Dakta Bukola Saraki sun zafafa yunkurin da ake zarginsu na karkatar da shugabancin jam'iyyar tare da datse bukatar dan takarar shugaban kasa daga kudanci.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa

Atiku da Saraki na kitsa kwace PDP daga gwamnoninta, su sake dawo da Secondus
Tsohon Shugaban PDP, Uche Secondus | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Masoyan Atiku da Saraki sun ce suna shirin karbe shugabancin jam’iyyar domin su mika takarar shugabancin kasa zuwa Arewa a 2023.

Wani bangare na shirin su shi ne za su shigar da kara a kotu kan jam'iyyar don tabbatar da dawowar tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus.

A halin da ake ciki, shugabannin kudanci na jam'iyyar sun karkatar da kananan ofisoshi da zuwa yankinsu.

Yayin da kudu maso yamma za ta sami mukaman sakataren jam'iyya na kasa da shugabar mata ta kasa, kudu maso gabas kuwa za ta sami mukaman sakataren yada labarai na kasa, sakataren kudi na kasa, da mataimakin sakataren kasa.

Dangane da tsarin karba-karba, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa kuma mai binciken kudi na kasa za su fito daga kudu maso kudu.

Kara karanta wannan

Ya zama dole a ba yankin Kudu takarar shugaban kasa a zaben 2023 inji Jigon PDP

Takaddama ta kunno kai tsakanin shugabannin kudu kan wasu mukamai 11 a PDP

Wani rahoto da jaridar The Nation yana nuna cewa wani sabon rikici na kunno kai a jam'iyyar PDP bayan shawarar da shugabannin jam'iyyar suka yanke na mayar da mukamin shugabanta na kasa zuwa Arewacin Najeriya.

An yanke shawarar karkatar da ofishin ne ba tare da fayyace ko tikitin takarar shugaban kasa na 2023 na jam'iyyar zai karkata zuwa kudu ko a bude ga kowa ba.

A cewar rahoton, shugabanni da jiga-jigan PDP na shiyyar kudancin a yanzu sun shiga sabani kan abubuwan da ke faruwa.

Tare da matsayin shugaban jam'iyyar a Arewa, duk sauran mukaman kwamitin aiki na kasa (NWC) na jam'iyyar a halin yanzu a kudanci suma za a ba da su zuwa Arewa.

A bangare guda, duk mukaman da 'yan Arewa ke rike da su a yanzu 'yan kudu za su iya yin takararsu nemansu ne kadai a nan gaba.

Kara karanta wannan

Takaddama ta kunno kai tsakanin shugabannin kudu kan wasu mukamai 11 a PDP

Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

A tun farko, Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba ya amince da karkatar da matsayin shugaban jam’iyyar zuwa Arewa.

Hukuncin ya biyo bayan amincewa da shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin karba-karba na babban taron jam’iyyar PDP na kasa wanda gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ke jagoranta.

Kwamitin karba-karba na Ugwuanyi ya musanya shugabanci da duk wasu mukamai na zababbun jam’iyyun da mutanen Arewa ke rike da su yanzu da na Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel