Ya zama dole a ba yankin Kudu takarar shugaban kasa a zaben 2023 inji Jigon PDP

Ya zama dole a ba yankin Kudu takarar shugaban kasa a zaben 2023 inji Jigon PDP

  • Bode George yana cikin masu goyon bayan mulki ya koma Kudu a zaben 2023
  • George yace dole ne a ba ‘Yan Kudu takarar shugaban kasa saboda ayi adalci
  • A cewarsa yanki guda ba zai tattara shugaban jam’iyya da shugaban kasa ba

Lagos - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Olabode George ya soki tsarin da jam’iyyar hamayya PDP ta dauka game da zabe mai zuwa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Bbode George ya na cewa matakin da ake neman dauka na cewa a bar kowane yanki ya nemi shugaban kasa, yana da hadari.

George yana da ra’ayin cewa tun da an ba yankin Arewacin Najeriya kujerar shugaban jam’iyya, abin da ya dace shi ne a ba yankin Kudu tutan takara a 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon APC yace ‘Yan Najeriya su shiryawa bakar wahala bayan ganin kasafin 2022

A wani jawabi mai taken “Zoning is about equity and fairness” da jagoran na PDP ya fitar, ya nuna goyon bayansa ga tsarin karba-karba a wajen rike mukamai.

Jaridar ta rahoto George yana cewa ya kamata PDP ta maida mulki zuwa Kudu a zaben 2023.

'Yan PDP
PDP na kamfe a Katsina Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bode George yace wannan dadadden tsari ne a PDP

“Akwai tsohon tsarin da shugabanninmu da suka kafa PDP tun 1999 suka kawo, suka ce dole wasu kujeru su rika zagaya wa tsakanin bangarori shida domin adalci.”
“Wadannan kujeru su ne na shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, shugaban majalisar wakilai da sakataren gwamnatin tarayya.”
“Hakan yana nufin idan shugaban kasa ya fito daga yankin Arewacin Najeriya, sai shugaban jam’iyya ya fito daga yankin Kudancin Najeriya ko kuma akasin haka.” - Bode George

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

A cewar Bode George, ana yin wannan kaso ne saboda mutanen kowane yanki su ji cewa ana yi da su, yace ya zama dole a rika tafiya tare da kowa wajen shugabanci.

Kusan na PDP yace wannan ne turken da ya rike PDP tun 1999, amma yanzu ana yi wa wannan tsari barazana domin barin kofar takara a bude zai haddasa da rikici.

Ba a yi wa 'da dole a siyasa - Sule Lamido

Kwanakin baya aka ji Sule Lamido ya yi tir da matsayar da gwamnonin Kudu suka dauka kan 2023. 'Dan siyasar yake cewa ba za a kai mulki Kudu saboda son rai ba.

Da aka yi wata hira da shi, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya fada wa gwamnonin cewa ba a yin dole a siyasa, kamar yadda wasu suke cewa ne dole mulki ya bar Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel