Takarar shugaban ƙasa a 2023: Gwamna ya fara ziyarar neman shawara a Arewa, ya dira fadar sarkin Zazzau

Takarar shugaban ƙasa a 2023: Gwamna ya fara ziyarar neman shawara a Arewa, ya dira fadar sarkin Zazzau

  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya gana da shugaban ƙungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi
  • Gwamna Bello ya gana da shi domin neman shawara kan kudurinsa na neman takara a zaɓen 2023
  • Farfesa Abdullahi, yace gwamna Yahaya Bello, tamkar ɗa ne a wurinsa domin kawunsa abokin karatunsa ne

Zaria - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya gana da shugaban ƙungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi a Zariya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya gana da Farfesan ne domin neman shawara kan kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023.

Hakanan kuma Yahaya Bello ya ziyarci sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamali, a fadarsa dake birnin Zariya.

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello
Takarar shugaban ƙasa a 2023: Gwamna ya fara ziyarar neman shawara a Arewa, ya dira fadar sarkin Zazzau Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gwamna Bello ya faɗawa manema labarai bayan taron cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

An yi taron murnar dawowar Tinubu Najeriya, ya magantu kan tafiya da dawowarsa

"Zuwa na Zariya yau tamkar na dawo gida ne. A nan na tashi, na yi ilimi anan, suka tarbiyyantar dani anan, kafin subar ni na koma Kogi."
"Na kawo ziyara gida ne domin neman shawara, yan Najeriya na bukatar mu jagorance su, saboda haka ya kamata na nemi shawarar manya na, waɗanda suka ga jiya suka ga yau."

Bello ya ziyarci fadar sarkin Zazzau

Yayin ziyararsa fadar mai martaba sarkin Zazzau, Gwamna Yahaya yace:

"Shekara ɗaya kenan da naɗin sarkin Zazzau, muna amfani da wannan damar wajen taya shi murnar cika shekara ɗaya a kujerar mulki."
"Zariya gida na ne kuma makotan mu ne, ban samu zuwa bikin naɗi ba, sai dai wakili na, amma yau gani nazo taya murna da neman goyon baya."

Yahaya ɗan mu ne - Farfesa Ango

Shugaban ƙungiyar dattawan Arewa, Ango Abdullahi, ya bayyana cewa gwamna Yahaya Bello tamkar ɗa ne a wurinsa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Babban Sarki a Arewa, Dr Shekarau Agyo, ya riga mu gidan gaskiya

Farfesa Ango yace:

"Kawunsa abokin karatu na ne shekaru 70 nan baya, saboda haka zan yi mamaki idan aka ce mun ya zo Zariya bai kawo mun ziyara ba."
"Ya zo nan ne ya faɗa mun kudirinsa wanda ya riga ya fara, kudirin neman kuri'un yan Najeriya na zama shugaban ƙasa. A takaice yazo neman shawara ne."

A wani labarin kuma kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shine abin damuwa ba.

Atiku yace babu wani abu shugaban ƙasa daga kudu ko daga arewa, abinda duniya ta sani shine shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel