Buhari: Mu na da sabbin makaman yakar kowanne irin rashin tsaro

Buhari: Mu na da sabbin makaman yakar kowanne irin rashin tsaro

  • Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya ta samu sabbin makamai na yakar rashin tsaro
  • A cewarsa, an kawo makaman kasar nan kuma za a tura su dukkan sassan kasar nan domin yakar kowanne nau'in rashin tsaro
  • A yayin yayen hafsoshin soji da aka yi a Kaduna, Buhari ya ce ya na kan bakansa wurin yaki da rashawa a kasar nan

Kaduna - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar nan ta samu sabbin makamai da za ta iya yakar kowanne nau'in rashin tsaro, TheCable ta ruwaito.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin bikin yaye daliban aji na 68 da suka hada da hafsoshin sojin kasa, ruwa da na sama da aka yi a makarantar horar da hafsoshin soji ta NDA da ke Kaduna.

Read also

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

Buhari: Mu na da sabbin makaman yakar kowanne irin rashin tsaro
Buhari: Mu na da sabbin makaman yakar kowanne irin rashin tsaro. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

Shugaban kasan ya bayyana damuwarsa kan rashin tsaro inda ya ce ya sakankance cewa sabbin kayan aiki da aka kawo za su matukar taka rawa wurin inganta tsaro a kasar nan, TheCable ta wallafa.

"Kamar yadda ku ka sani, kasar Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro a wannan lokacin. Muna cigaba da fuskantar barazana da tashin-tashina ta bangarne ta'addanci, 'yan fashin daji, garkuwa da mutane da kashe-kashen da 'yan siyasa suke sa wa wanda ya ke barazana ga hadin kan kasar nan," yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina tabbatar muku da cewa wannan mulkin zai cigaba da yin duk abinda ya dace wurin dabba'a doka tare da kawar da duk wan nau'i na rikici da ke samar da tsoro da tashin hankali a zukatan 'yan kasar nan.
“Akwai matukar amfani in sanar da ku cewa mun samu sabbin makaman yakar kowanne rashin tsaro daga kasar nan. Wadannan kadarorin za a tura su wurare daban-daban domin yakar rashin tsaro a dukkan sassan kasar nan."

Read also

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

Shugaban kasan ya kara da cewa, mulkinsa har yanzu ya na kan bakansa na yaki da kalubalen rashin tsaro, rashawa da kuma tattalin arziki.

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

A wani labari na daban, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya ziyarci garin Banki a ranar Alhamis, gari da ya ke kusa da iyakar Najeriya da Kamaru, inda suka ci kasuwar dare bayan shekaru bakwai da rufe ta saboda ta'addanci.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tare da rakiyar wasu jami'an gwamnati, Zulum ya ziyarci wasu manyan shaguna wurin karfe goma da rabi na dare.

An gano cewa ya je tare da duba yadda garin ke habaka da al'amuran rayuwa da na tattalin arziki, hakan yasa ya kwatanta abinda ya gani da lokaci mafi farin ciki a rayuwarsa tun bayan hawansa gwamna.

Source: Legit.ng News

Online view pixel