Gwamna Sani Bello ya mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kontagora, Alhaji Mohammed Barau Kontagora

Gwamna Sani Bello ya mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kontagora, Alhaji Mohammed Barau Kontagora

  • Gwamna Abubakar Sani Bello ya mika wa sabon sarkin masarautar Kontagora, Alhaji Mohammed Barau Kontagora takardar kama aiki
  • An yi taron mika takardar ne gidan gwamnati da ke Minna, babbar birnin jihar Neja
  • Gwamnan ya roki sabon Sarkin da ya tafi da kowa, don tabbatar da zaman da ci gaban masarautar

Gwamna Abubakar Sani Bello ya mika wa sabon zababben sarkin masarautar Kontagora, Alhaji Mohammed Barau Kontagora takardar kama aiki.

An gudanar da taron gabatarwar ne a gidan gwamnati da ke Minna, babbar birnin jihar Neja.

Gwamna Sani Bello ya mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kontagora, Alhaji Mohammed Barau Kontagora
Gwamna Sani Bello ya mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kontagora, Alhaji Mohammed Barau Kontagora Hoto: Office Of The Chief Press NGS - Mary Noel Berje
Asali: Facebook

Gwamna Bello wanda Kwamishinan Kananan Hukumomi, Cigaban Al'umma da Al'amuran Masarautu, Mista Emmanuel Umar ya wakilta ya roki sabon Sarkin da ya tafi da kowa, don tabbatar da zaman lafiya wanda yace ya zama dole don ci gaban masarautar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sake kai wa Rimingado 'farmaki', 'yan sanda na shirya sabbin tuhuma

Ya tunatar da Sarkin aikin da ke gabansa, lura da cewa ya hau kan kujerar kakanninsa a cikin mawuyacin lokaci na rashin tsaro da ke addabar jihar ciki har da Masarautar sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da sakatariyar yada labaran gwamnan, Mary Berge ta saki ta ce gwamnan ya kuma roki Allah da ya ba shi hikimar jagorantar talakawansa ta hanya madaidaiciya.

Ya yi addu'a ga nasarar masarautar Kontagora a karkashin sabon sarkin kuma ta sami ci gaba da zaman lafiya.

Ya ce:

"Na gode wa Allah ga mutanen Masarautar Kontagora wadanda suka yi imani da gwamnati sannan kuma suka yi duk abin da ya kai ga wannan toro.
"Ko da yake ya zo ne a mawuyacin lokaci, ina addu'ar Allah ya albarkaci mulkinsa, ya ba da zaman lafiya a kasar. A lokacin mulkinsa, Kontagora zai yi fure."

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

Sabon Sarkin Sudan na masarautar Kontagora, Alhaji Mohammed Barau Kontagora ya godewa Allah Madaukakin Sarki saboda zabar sa a cikin mutane da yawa don zama Sarki na 7 na Masarautar Kontagora.

Sarkin na 7 wanda ya ba da tabbacin cewa zai aiwatar da budaddiyar manufa, ya yi kira ga mutanen Masarautar da su kwantar da hankalinsu tare da yin alkawarin ciyar da Masarautar gaba.

Ya ce zai fara yin sulhu da duk wadanda suka yi takara da shi da nufin samar da zaman lafiya tare da yin aiki tare don ci gaban masarautar.

Nadin sabon sarkin ya biyo bayan rasuwar marigayi Mai Sudan, Alhaji Saidu Namaska ​​wanda ya rasu a ranar 9 ga Satumba, 2021 bayan shekara 47 a kan karagar mulki.

Bayan tirka-tirka, an zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Kontagora

A baya mun kawo cewa bayan tirka-tirka da rikice-rikice a Masarautar Kontagora, an sanar da Muhammad Barau Kontagora a matsayin sabon Sarkin Sudan na Kontagora.

Kara karanta wannan

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

Kwamishanan kananan hukumomi da lamuran masarautun gargajiya, Emmanuel Umar, ya bayyana hakan a jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Mary Berge ta saki ranar Laraba.

Kwamishanan ya bayyana cewa lallai zaben da akayi tun farko ya bi ka'ida kuma gwamnan jihar ya rattafa hannu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel