Zamu fara tilastawa ma'aikatan gwamnati yin allurar rigakafin Korona, SGF Boss Mustapha

Zamu fara tilastawa ma'aikatan gwamnati yin allurar rigakafin Korona, SGF Boss Mustapha

  • Gwamnatin tarayya na kan bakanta na wajabtawa yan Najeriya yin allurar rigakafin Korona
  • Gwamnati tace yanzu dai zata fara da ma'aikatan gwamnati
  • Bisa tsari, za'a tsirawa mutum allurar sai biyu da tazarar akalla kwanaki 21
  • Sabon Bincike a Amurka yanzu ya nuna cewa sai an tsira sau uku zai bada kariya sosai

Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata tilastawa ma'aikatan gwamnatin yin rigakafin Korona.

Yace amma ba za'a wajabtawa gama-garin yan Najeriya yin allurar rigakafin har si an samar da isasshen rigakafi da kowa zai samu.

Boss Mustapha ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da kwamishanonin lafiya na jihohin Najeriya a Abuja, rahoto Punch.

Zamu fara tilastawa ma'aikatan gwamnati yin allurar rigakafi COVID-19, SGF Boss Mustapha
Zamu fara tilastawa ma'aikatan gwamnati yin allurar rigakafin Korona, SGF Boss Mustapha Hoto: PR
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

Yace:

"Ko shakka babu za'a tilastawa mutane yin allurar rigakafin Korona. Muddin kasashen Turai suka gama yiwa al'ummarsu rigakafin Korona, ba za ka iya zuwa ba sai ka yi. Wannan tuni ya fara faruwa."
"Dalilin da yasa zamu wajabtawa ma'aikatan gwamnati yin rigakafin shine zasu rika tafiye-tafiye a madadin gwamnatin tarayya."
"Za mu bi abin daki-daki. Ba zamu iya wajabtawa gama-garin jama'a yanzu ba har sai mun tabbatar da cewa akwai isasshen rigakafin kuma an tura ko ina da mutane zasu samu."
"Idan lokaci yayi, zamu wajabtawa kowa ko kuma ba zamu bari mutum ya shiga wani ofishi na gwamnati ba."

Tilastawa kowa yin rigakafin Korona: Wannan ya sabawa hankali, Likitoci sun caccaki gwamnati

Kungiyar Likitocin Najeriya NMA da kungiyar ma'aikatar kiwon lafiya karkashin gamayyar ma'aikatan asibiti (JOHESU) sun yi martani kan shirin wajabtawa yan Najeriya yin rigakafin Korona.

Yayinda NMA tace mutane na da hakkin cewa ba zasu yi rigakafi ba, sauran ma'aikatan lafiya sun ce wannan shirin tilastawa mutane yi ya saba hankali.

Kara karanta wannan

Tilastawa kowa yin rigakafin Korona: Wannan ya sabawa hankali, Likitoci sun caccaki gwamnati

Kakakin gamayyar JOHESU, Mr Olumide Akintayo, a hirar da yayi da jaridar Punch ya yi Alla-wadai da gwamnonin dake kokarin wajabta yiwa mutane allurar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng