Xavi, Andrea Pirlo, da koci 7 da za su iya maye gurbin Ronald Koeman a Barcelona

Xavi, Andrea Pirlo, da koci 7 da za su iya maye gurbin Ronald Koeman a Barcelona

  • Ana rade-radin za a sallami Ronald Koeman daga aikinsa a kungiyar Barcelona
  • Daga cikin wadanda ake gani za su iya gadon kujerarsa akwai Xavi Hernandez
  • An kara huro wa Koeman wuta ganin yadda kungiyar ta ke samun rashin nasara

Barcelona - Antonio Conte da Andrea Pirlo suna cikin wadanda kungiyar Barcelona ta ke hari a matsayin sabon koci idan aka sallami Ronald Koeman.

A ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021, Sun tace Ronald Koeman yana fuskantar barazana a Nou Camp a sakamakon halin da Barcelona ta ke ciki.

Xavi zai dawo?

Jaridar tace daga cikin wadanda kungiyar ta ke tunanin dauko haya a matsayin mai horas da wasanta akwai tsohon ‘dan kwallonta, Xavi Hernandez.

Xavi yana horas da kungiyar kasar Qatar, Al Sadd a halin yanzu, kuma tun a shekarun baya ake ta rade-radin zai dawo Barcelona a matsayin kocin ‘yan wasa.

Kara karanta wannan

Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi

Rahoton ya kuma ce tsohon kocin Juventus da Chelsea, Antonio Conte zai iya zama sabon kocin Barcelona. A karshen kakar bana kocin ya bar kungiyar Inter.

Xavi yana horas da kungiyar kasar Qatar, Al Sadd a halin yanzu, kuma tun ba yau ba ana ta rade-radin zai dawo kungiyar da ya bari a 2015 a matsayin koci.

Ronald Koeman
Kocin Barcelona, Ronald Koeman Hoto: metro.co.uk
Asali: UGC

Wani suna da yake yawo a Barcelona shi ne Andrea Pirlo wanda kungiyar Juvenuts ta kora kwanaki.

Pirlo ya rasa aikinsa duk da ya yi nasarar lashe gasar Coppa Italia da Supercoppa Italiana. Shi kuma Conte ya ajiye aiki bayan Inter ta zama zakarar Italiya.

‘Dan jaridar nan na Sifen, Gerard Romero, yace Koeman mai shekara 58 zai iya ganin kujerarsa ta koma hannun tsohon kocin kasar Jamus, Joachim Low.

Kara karanta wannan

Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP

Jaridar Sportsmole tace kungiyar kwallon kafan za ta biya fam Dala miliyan 10 muddin ta sallami kocinta, Koeman kafin wa’adinsa ya cika a shekarar 2022.

Wasu koci 5 da ake magana

A wani kaulin ana ambatan sunayen kocin da ba su yi fice ba irinsu Jordi Cruyff, Sergi Barjuan, Erik Ten Haag, da Roberto Martinez da kuma Henrik Larson.

Lionel Messi ya tashi

A watannin baya ne fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya, Lionel Messi, ya bar Barcelona, ya kulla yarjejeniya da PSG a kan kwantaragin shekaru biyu.

A halin yanzu Barcelona tana matsayi na bakwai ne a La-liga bayan ta sha da kyar a hannun Granada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel