Sarakunan gargajiya 65 sun yi wa Asiwaju Tinubu mubaya’a ya zama Shugaban kasa a 2023

Sarakunan gargajiya 65 sun yi wa Asiwaju Tinubu mubaya’a ya zama Shugaban kasa a 2023

  • Sarakuna sama da 60 a jihar Legas suna goyon bayan takarar Bola Tinubu
  • Sarkin Igando Lasisi Gbadamosi yace za su mara wa tsohon gwamnan baya
  • Sarakunan sun yi wannan bayani yayin da suka gana da kungiyar SWAGA

Lagos - Shugaban sarakunan gargajiya na reshen Ikeja, Legas, Sarki Lasisi Gbadamosi yace sarakuna 65 a yankinsa sun yi wa Asiwaju Bola Tinubu mubaya’a.

Mai martaba Lasisi Gbadamosi wanda shi ne Onigando na kasar Igando ya bayyana wannan a lokacin da kungiyar nan ta SWAGA 2023 ta ziyarce su a garin Ikeja.

South-West Agenda (SWAGA) for “Bola Tinubu 2023 mai yi wa Tinubu kamfe ta gana da Sarakunan ne a kokarin ta na ganin tsohon gwamnan ya samu mulki.

Jaridar PM News ta rahoto Sarki Lasisi Gbadamosi yana cewa Bola Tinubu ya fi kowa dace wa ya nemi shugaban kasa, ya yi masa fatan ya samu nasara a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Mai martaban yake cewa Asiwaju Bola Tinubu zai karbi mulki, kuma Sarakuna za su mara masa baya.

Sarakunan gargajiya
Wasu sarakunan Yarbawa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rilwan Akiolu yana tare da sauran Sarakunan Legas

Vanguard tace Sarkin Legas, Rilwan Akiolu ya goyi bayan wannan ra’ayi a taron, yace tsohon gwamnan na jihar Legas ya fi dace wa ya gaji Muhammadu Buhari.

Oba Tijani Akiloye wanda ke rike da sarautar Ajiran na kasar Ajiranland a garin Eti-Osa, shi ne ya wakilci Akiolu a taron, yace Sarakunan Legas suna goyon bayansa.

Kyau mulki ya koma Kudu - Adedayo Adeyeye

Shugaban kungiyar magoya bayan na Bola Tinubu, Adedayo Adeyeye, ya goyi bayan kiran da ake yi na tsaida ‘dan takarar shugaban kasa daga kudancin Najeriya a 2023.

Sanata Adedayo Adeyeye yace damka wa ‘dan kudu tikitin shugaban kasa zai kawo zaman lafiya a kasar.

Kara karanta wannan

Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023

Tsohon Ministan yake cewa ware wa kudu mulki bai nufin yankin kudu maso yamma kadai za su samu damar takara, yace sauran bangarori na iya neman shugabanci.

Ba za ayi wa wani dole a 2023 ba - Sule Lamido

A jiya aka ji tsohon gwamnan jihar Jigawa ya fada wa gwamnonin Kudu cewa ba a yin dole a siyasa. Hakan na zuwa ne bayan sun ce dole a ba su mulki a zaben 2023.

Sule Lamido yace jam'iyyar PDP ba za ta ba Kudu takarar Shugaban kasa da karfi da yaji ba. Sule yake cewa ana bada mulki ne idan an har ga hakan shi ne mafita a siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel