Da duminsa: Majalisar dattawa na barazanar bada umarnin damko Marwa da Monguno

Da duminsa: Majalisar dattawa na barazanar bada umarnin damko Marwa da Monguno

  • Majalisar dattawa na barazanar bayar da umarnin damko shugaban NDLEA, Buba Marwa da NSA Babagana Monguno
  • Majalisar ta ce ta tura wa ofishin NSA da hukumar NDLEA gayyata amma har yanzu shiru ka ke ji babu labari
  • Majalisar na zargin NDLEA da yin sama da fadi da wasu kudi har N467 miliyan, sai ofishin NSA da ake zargi da lamushe N3.5 biliyan

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta yi barazanar bayar da umarnin damko shugaban hukumar MDLEA, Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya da kuma mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Munguno, kan kin amsa gayyatarsu da suka yi.

Daily Trust ta wallafa cewa, Ofishin odita janar na tarayya ya mika tuhuma kan NDLEA da ofishin NSA a wani rahoto na 2016, wanda kwamitin majalisar kan asusun gwamnati ya duba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Da duminsa: Majalisar dattawa na barazanar bada umarnin damko Marwa da Monguno
Da duminsa: Majalisar dattawa na barazanar bada umarnin damko Marwa da Monguno
Asali: Original

An mika tuhuma 11 ga NDLEA kan lamurra da suka hada da watanda da kudade da za su kai miliyan N467, Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton kudin ya zargi cewa an aikata almundahanar ne a shekarar 2015 kafin a nada Marwa a matsayin shugaban hukumar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ofishin NSA Monguno kuwa, ana zarginsu da waskar da kudi da suka kai N3.5 biliyan da aka ware na siya ababen hawan hafsoshin sojoji.

Sanata Mathew Urhoghide, wanda ke shugabantar kwamitin majalisar wurin bincikar zargin, ya ce jami'ai daga dukkan hukumomin ba su amsa gayyatar da aka mika musu ba domin su yi bayani kan zarginsu.

Urhoghide ya sha alwashin cewa majalisar dattawan za ta yi amfani da karfin ikon da kundun tsarin mulki ya bata wurin tirsasa Marwa da Monguno su bayyana a gaban kwamitin.

Kara karanta wannan

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

"Ba mu duba girman mutum domin babu wanda ya gagare mu. Muna shawartarsu da su bayyana a gabanmu. Muna jan kunnensu a karo na karshe, za mu yi amfani da karfin ikon da kundun tsarin mulki ya ba mu wurin tirsasa su domin bayyana a gabanmu," yace.
A bangaren ofishin NSA, ya ce "NSA ya zo da kan shi domin karin bayani. Ba mu da wata matsala kai tsaye da shi. Mun bukaci ya turo wani ko kuma ya zo da kan shi."

NDLEA ta ce ba ta san da labarin gayyatar ta da aka yi ba daga majalisar dattawan.

Kotu ta yi fatali da bukatar Ndume ta zare hannunsa daga shari'ar Maina

A wani labari na daban, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja a ranar Litinin ta yi watsi da bukatar da sanata Ali Ndume ya mika gabanta na son zare kan shi a matsayin tsayayyen Abdulrasheed Maina, bayan ya tsallake sharuddan beli.

Kara karanta wannan

Tashar Africa Magic ta DSTV na shirin wasan kwaikwayo kan uwargidar Buhari

Mai shari'a Okon Abang a hukuncin da ya yanke bayan bukatar da Ndume ya shigar gaban ta, ya ce hakan tamkar cin zarafin kotu ne ganin cewa ya mika irin wannan bukatar gaban kotun daukaka kara a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, ya tsallake beli bayan an sako shi daga gidan gyaran hali na Kuje inda ya kwashe kusan watanni 9 bayan an gurfanar da shi a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel