Jami'an yan sandan sun damke mata masu kaiwa yan bindiga makamai a jihar

Jami'an yan sandan sun damke mata masu kaiwa yan bindiga makamai a jihar

  • Yan sanda sun damke mata masu kaiwa yan bindiga makamai
  • Yan matan biyu sun bayyana yan bindigan da suke kaiwa makamai
  • Kakakin hukumar yan sanda ya bayyana wasu barayin mota kuma

Abuja - Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun damke wasu yan mata biyu masu kaiwa tsagerun yan bindigan da suka addabi mutan Arewacin Najeriya makamai.

Kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, ya ce matan masu suna Aisha Ibrahim da Hafsat Adamu sun kasance masu kaiwa yan bindigan makami duk lokacin da suke bukata, PRNigeria ta ruwaito .

Daya daga cikinsu Aisha tace:

"Wasu lokuta akan bamu makamai daga Lafia ku ka Kaduna kuma ina samun nasaran kaiwa wani Babangida, wani dan bindiga."

Ita kuwa Hafsat, ya bayyana cewa tana kaiwa yan bindiga makamai Kaduna daga Kujama, bisa umurnin wani Suleiman.

Read also

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an yan sandan sun damke mata masu kaiwa yan bindiga makamai a jihar
Jami'an yan sandan sun damke mata masu kaiwa yan bindiga makamai a jihar Hoto: PRNigeria
Source: UGC

Hukumar ta bayyana shahrarrun barayin mota

Har ila yau, yan sandan sun damke wasu barayin da suka kware wajen satan mota a Kaduna, Kano da Jigawa, inda suke kaiwa kasashen Nijar, Kamaru da Chadi.

Kakakin hukumar yan sanda, CP Frank Mba yace an kwato na'urorin bude mota biyu, wanda ke taimaka musu wajen bude motocin da kuma lalata fasahar bibiyar mota.

Wadannan barayi sun hada da maza 32, da mata 2.

An damke Likitan yan bindiga a jihar Katsina, ya bayyana dalilin da yasa yake musu aiki

A bangare guda, Wani ma'aikacin lafiya a jihar Katsina, Murtala Umar, ya bayyana yadda ya kasance mai kula da yan bindiga yayinda suka samu raunuka duk da cewa ya san yan ta'adda ne.

Read also

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

A ranar Litinin, hukumar yan sanda a jihar Katsina ta gabatar da shi gaban manema labarai a hedkwatar hukumar, rahoton Premium Times.

Malamin jinyan mai suna Murtala ya bayyanawa manema labarai cewa dole ce ta sa shi yake aiki da su. Murtala na da shagon sayar da magunguna a Tashar Yar Alewa, dake karamar hukumar Danmusa.

Source: Legit

Online view pixel