An damke Likitan yan bindiga a jihar Katsina, ya bayyana dalilin da yasa yake musu aiki
- Yan sanda sun damke mai kula da lafiyan tsagerun yan bindiga a Katsina
- Matashin ya bayyana cewa shi ke sayar musu da maguna kuma yake musu jinya
- Ya yi nadamar abinda yayi kuma idan aka yafe masa ba zai sake ba
Katsina - Wani ma'aikacin lafiya a jihar Katsina, Murtala Umar, ya bayyana yadda ya kasance mai kula da yan bindiga yayinda suka samu raunuka duk da cewa ya san yan ta'adda ne.
A ranar Litinin, hukumar yan sanda a jihar Katsina ta gabatar da shi gaban manema labarai a hedkwatar hukumar, rahoton Premium Times.
Malamin jinyan mai suna Murtala ya bayyanawa manema labarai cewa dole ce ta sa shi yake aiki da su.
Murtala na da shagon sayar da magunguna a Tashar Yar Alewa, dake karamar hukumar Danmusa.
Al'ummar garin ne suka sanar da yan sanda yayinda suka zargi abinda yake yi.
Yace:
"Na yi karatu a Kwalejin kiwon lafiya da fasaha dake Kankia amma ban fara aiki ba. Yan bindigan na zuwa shagona don neman taimako kuma su biya ni."
Yace yana sane da cewa yan bindiga ne saboda suna zuwa da bindigoginsu, amma babu yadda ya iya da su.
Ya bayyana cewa "yayi nadamar abinda yayi kuma ba zai sake ba."
An damke wasu mata masu kaiwa yan bindiga man fetur a jihar Katsina
Hukumar yan sanda a jihar Katsina ranar Alhamis ta damke wasu mata uku da ake yiwa zargin kaiwa yan bindiga man fetur cikin daji a jihar.
Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, a hira da manema labarai a Katsina, ya bayyana matan uku; Dija Umar, 50; Ummah Bello, 45; da Nusaiba Muhammad, 16 yan unguwar Malali, a cikin Katsina.
Kakin yan sandan yace an damke su ne a titin Katsina zuwa Jibiya.
Asali: Legit.ng