Tsohon Kwamishina ya yi magana bayan Mai dakin Ganduje ta shiga hannun Jami'an EFCC

Tsohon Kwamishina ya yi magana bayan Mai dakin Ganduje ta shiga hannun Jami'an EFCC

  • Mu’az Magaji ya yi magana a kan tirkar-tirkar Hafsat Ganduje da hukumar EFCC
  • Tsohon Kwamishinan ya yi wasu maganganu a kan batun a shafinsa na Facebook
  • Dansarauniya ya nuna yaron Gwamna bai kyauta da ya kai kara wajen EFCC ba

Kano - Mu’az Magaji wanda aka sani da ‘Dansarauniya ya tofa albarkacin bakinsa a kan gayyatar da EFCC ta yi wa mai dakin gwamnan Kano, Hafsat Ganduje.

Injiniya Mu’az Magaji ya yi magana a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2021, inda aka ji yana nuna Abdulaziz Ganduje bai kyauta ba.

“Gaskiya yaron nan Abdulazeez Garo bai kyauta mana ba.” - inji Dansarauniya

Ko da bai kama suna ba, ana kyautata zaton Dansarauniya yana nufin Abdulaziz Abdullahi Ganduje wanda ya kai karar mahaifiyarsa wajen jami’an EFCC.

Read also

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

Kafin nan, a safiyar yau, Dansarauniya wanda yake jagorantar tafiyar siyasar Win-Win a Kano ya wallafa labarin gayyatar da EFCC tayi wa uwargidar mai gidansa.

Ba wannan ne karon farko da Mu’az Magaji ya caccaki Abdulaziz Ganduje a shafinsa ba, akwai lokacin da aka ji yana cewa tun can ba ya tare da gwamnatinsu.

Hafsah Ganduje
Mai dakin Gwamnan Kano, Hafsah Ganduje Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Ba zan sake magana ba

Daga baya sai tsohon kwamishinan ayyukan na jihar Kano ya fito yace ba zai sake cewa uffan ba.

“No comment on that matter again! Mu je zuwa! Kanon Dabo, Birni…”

Kawo yanzu mutane suna ta maida wa Injiniya Magaji martani a dandalin sada zumuntan na Facebook. Kalaman da ya yi, sun jawo ana tofa albarkacin baki.

A nan ne wani abokinsa a kafar Facebook, Aliyu Isa Aliyu ya maida masa martani yace tsohon kwamishinan yana tsoron yin abin da zai sake jawo masa matsala.

Read also

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

“Duk abin da ya san zai ja masa matsala a siyasance komin gaskiyar abun, zai guje sa. Babu maganar don al’umma yake gwagwarmaya.” - Aliyu Isa Aliyu.

Idan za a tuna gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige Magaji daga Kwamishina ne bayan wasu maganganu da yayi a shafin Facebook bayan mutuwar Abba Kyari.

Me gwamnatin Kano ta ke fada?

Dazu aka ji Gwamnatin Jihar Kano ta maida martani kan rahotannin da yake yawo cewa an cafke matar Gwamna Abdullahi Ganduje, tace batun ba gaskiya ba ne.

A wata sanarwa, Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, yace ba za a iya bin diddigin labarin da ba shi da asali daga wata tushe ba.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel