Shekara 30 yayi yana sharan Masallaci, ko aure bai taba yi ba: Adamu Yakubu kan Malam Musa

Shekara 30 yayi yana sharan Masallaci, ko aure bai taba yi ba: Adamu Yakubu kan Malam Musa

  • Allah ya yiwa Malam Musa Mai Shara da kiran Sallar Farko na Asuba a Masallacin Sultan Bello rasuwa
  • Mutane da dama na tofa albarkatun bakinsu kan dattijon
  • Dattijon ya rasu ne a asibitin Barau Dikko dake jihar Kaduna

Kaduna - Malam Adamu Yakubu ya bayyana irin rayuwar da Malam Musa Jos, Dattijon arziki, wanda ya shahara a babban Masallacin Sultan Bello dake jihar Kaduna, yayi.

A sakon ta'azziyar da yayi, ya bayyana cewa Malam Musa gaba daya rayuwarsa na kullum a bautar Masallacin Sultan Bello yakeyi tun daga safe har rana.

A jerin shaidun alherin da yayi kan marigayin, ya bayyana cewa shekarun Malam Musa 30 da yin wadannan ayyukan Ibada kuma bai da wata sana'a illa wannan.

Read also

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

A cewarsa:

"Mal. Musa Abdullahi (kwarkwar) lafari ne daga Jos wanda ya kwashe shekaru 30 na rayuwarsa yana sharan Masallacin Sultan Bello."
"Wannan aiki yake tun daga safe har rana.A Masallaci yake rayuwarsa kuma bai da wani aiki da ya wuce Sallolin farilla biyar sannan kuma jefi-jefi yayi wa'azi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ko aure bai taba yi ba, abin duniya bai damesa ba

Adamu Yakubu ya cigaba da cewa Malam Musa ya gudanar da rayuwarsa ba tare da damuwa da abin duniya ba.

A cewarsa, ko aure dattijon bai taba yi ba.

Yace:

"Sau daya yake zuwa gida don ganin mahaifiyarsa kuma yayi mata kyauta. Bai taba aure ba, kuma bai taba damuwa da abin duniya ba."

Shekara 30 yayi yana sharan Masallaci, ko aure bai taba yi ba: Adamu Yakubu kan Malam Musa
Shekara 30 yayi yana sharan Masallaci, ko aure bai taba yi ba: Adamu Yakubu kan Malam Musa
Source: Facebook

Malam Musa Mai Shara da kiran Sallar Farko na Asuba a Masallacin Sultan Bello

Read also

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Dattijon arziki, Malam Musa Jos, wanda ya shahara a babban Masallacin Sultan Bello dake jihar Kaduna, ya rigamu gudan gaskiya.

Babban Malami, Sheikh Ahmad Gumi, ya sanar da hakan ne a shafinsa na Facebook da safiyar Litnin, 4 ga watan Oktoba, 2021.

A cewar Malam Gumi, marigayin ya kasance mai sharan Masallacin kuma mai kiran Sallar farko ta Asuba a Masallacin.

Source: Legit

Online view pixel