Boko Haram: ‘Yan ta’adda sun kafa daula a Neja, sun ce ayi watsi da umarnin Gwamnati da Boko

Boko Haram: ‘Yan ta’adda sun kafa daula a Neja, sun ce ayi watsi da umarnin Gwamnati da Boko

  • ‘Yan Boko Haram na neman hana jama’a sakat a wasu kauyukan jihar Neja
  • Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce sojojin na Boko Haram sun shigo masu
  • ‘Yan ta’addan suna kira ga wasu mazauna da suyi watsi da umarnin hukuma

Niger - Daily Trust tace wasu ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun shiga kauyuka da dama a kananan hukumomin da ke jihar Neja.

‘Yan ta’addan sun fara jan-kunnen mutane su cire ‘ya ‘yansu daga makarantun boko na zamani.

Rahotonni sun ce mazauna wadannan yankuna na jin tsoron rayuwarsu za ta iya shiga cikin hadari muddin ba a dauki mataki a kan wannan lamarin ba.

Ta’adin da ake yi a yankunan Neja ya zarce na ‘yan bindigan da ake ta fada. Haka zalika ana kai irin wadannan hare-hare a Kaduna, da Katsina da kewaye.

Read also

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

Me gwamnan Neja ya fada?

A ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, 2021, Mai girma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya bayyana cewa akwai ‘Yan Boko Haram a kauyukan Neja.

Abubakar Sani Bello
Gwamna Abubakar Sani Bello da Shugaban kasa Hoto: www.abusbello.com
Source: UGC

“Muna da duk wasu dalilai da za su sa mu yarda ba da ‘yan bindiga muke yaki ba. Yadda aka tsara hare-haren da aka kai a baya-bayan nan ya nuna haka.”
“Hakan ya nuna mana cewa wadannan sun samu horaswa na musamman.” – Gwamna Sani Bello.

An samu bama-bamai da wadannan ‘yan ta’adda suka shuka a yankin Shiroro. Hakan ya kara tabbatar wa gwamnati cewa ‘Yan Boko Haram sun shigo garin.

Boko Haram sun dade a Neja?

Tun bayan wasu hare-hare da aka kai a Shirororo da Munya a watan Afrilun 2021, gwamna Sani Bello ya shaida wa ‘yan jarida cewa aikin kungiyar Boko Haram ne.

Read also

Tsohon Kwamishina ya yi magana bayan Mai dakin Ganduje ta shiga hannun Jami'an EFCC

Boko Haram sun kafa tuta a kauyen Kaure, sun karbe iko da garin. Hakan na zuwa bayan sojojin Najeriya sun fatattaki mayakan Ansarul-Islam da na Darul-Salam.

A aurar da 'yan mata

Kafin nan an samu labari cewa ‘yan ta’addan da ake zargi ‘yan Boko Haram ne sun bukaci musulmai da kiristoci su aurar da duk yaran da suka kai shekara 12.

'Yan Boko Haram suna yaki da karatun boko da kuma barin mata da ake yi ba tare da aure ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel