2023: Abubuwa za su jagwalgwalewa Atiku, Kwankwaso da sauran ‘Yan takaran Arewa a PDP
Jam’iyyar PDP ta ba Arewa dama ta fito da sabon shugaban jam’iyya na kasa
Ana tunani hakan zai sa ‘yan siyasan yankin su rasa damar shiga takara a 2023
Watakila irinsu Atiku, Kwankwaso, Saraki na da shirin neman shugaban kasa
Abuja - Da alamu an rage wa ‘yan siyasar Arewa irinsu Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, da Aminu Waziri Tambuwal kwarin gwiwar takara a 2023.
Jaridar Daily Trust tace an canza wa ‘yan siyasan Arewa da ke sha’awar neman kujerar shugaban kasa a 2023 a jam’iyyar PDP lissafi bayan kason mukamai.
Kwamitin Ifeanyi Ugwuanyi ya kai kujerar shugaban ja’iyya zuwa Arewacin Najeriya. Hakan ya sa ake tunani PDP za ta ba ‘Dan kudu tikitin shugaban kasa.
Sauran wadanda ake tunani suna harin kujerar shugaban kasa a PDP sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da Sule Lamido.
‘Yan takara sun yi gum
Rahoton yace wadanda ake sa rai za su nemi tutar takarar shugaban kasa a PDP ba su ce komai ba tun bayan da kwamitin ya bayyana matsayar da ya dauka a jiya.
Da aka tuntubi shugaban PDP na jihar Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, sai yace ya kamata a bar ‘dan Arewa ya rike wa PDP tuta a zaben 023, idan har da adalci.
Za a bar kofa a bude?
A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba, 2021, tace akwai yiwuwar shugabannin jam'iyyar PDP su bar kofar neman tuta a bude.
Wani daga cikin manyan PDP ya shaida wa jaridar cewa da alamu Kudu za a kai takara a a 2023, amma yace tun da siyasa ce, yana yiwu wa 'dan Arewa ya samu tikiti.
Matsayar da kwamitin ya dauka sai ya je gaban majalisar koli ta NEC kafin jam’iyya ta amince da shi.
Kwamitin kasa mukamai da kujeru
Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ne aka ba aikin tsara yankin da kowane ‘dan takara zai fito a 2023, haka zalika yadda za ayi rabon mukaman jam’iyya.
A karshe kwamitin Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya ba yankin Arewacin Najeriya mukamin shugaban jam’iyya na kasa, akasin abin da ake tunani zai faru.
Ragowar ‘yan kwamitin sune Samuel Ortom na jihar Benuwai, da mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Aliyu Mohammed, wanda shi ne sakatarensu.
Asali: Legit.ng