Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi kasar Habasha domin halartan biki

Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi kasar Habasha domin halartan biki

  • Bayan killace kansa na mako guda, Buhari zai sake tafiya wata kasa
  • Buhari zai amsa gayyatan Firai Ministan Habasha wanda ya sake lashe zabe
  • Shugaban kasan zai tafi tare da Minista daya da shugaban hukumar NIA

Abuja - Bayan mako daya da dawowarsa daga kasar Amurka, shugaba Buhari ya kudirci niyyar sake shillawa kasar Habasha ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, 2021.

Shugaban kasan zai tafi halartan taron rantsar da Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed a wa'adinsa na biyu a Addis Ababa.

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya saki ranar Asabar.

Za'ayi bikin rantsarwan ne ranar Litnin 4 ga wata.

Daga nan kuma zai halarci liyafar cin abinci tare da sauran shugabannin ƙasashe sannan ya dawo ranar Talata.

Read also

Kano: Matashi mai shekaru 21 ya jagoranci fashi a gidan maƙwabcinsa

Daga cikin wadanda zasu yiwa Buhari rakiya akwai ministan harkokin waje Geoffery Onyeama da Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Tuni da shugaba Buhari ya aike sakon taya murna da Firai Ministan inda ya tabbatar masa da goyon bayan Najeriya.

Buhari yace:

"A madadin ya Najeriya, ina mika sakon taya murnata ga al'ummar Habasha bisa kokarinku wajen zabe kuma ina kira gareka ka cigaba da ayyukan kwarai ga al'ummarka."

Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi kasar Habasha domin halartan biki
Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi kasar Habasha domin halartan biki
Source: Facebook

Bankin duniya ya ja kunnen Najeriya kan ta guji kashe kudi mara amfani

A bangare guda, Bankin duniya ya shawarci Najeriya da sauran manyan kasuwanni da su datse kashe kudi mara amfani kuma su nemi gyararren tsarin bashi domin inganta tattalin arzikin jama'arsu.

Shugaban bankin, David Malpass, ya yi kira ga duniya kan hadin kai wanda ya hada da bangarori masu zaman kansu wurin samar da bashi ga kasashen duniya masu fama talauci, The Nation ta wallafa.

Read also

Da dumi: Yan majalisa sun kalubalanci Buhari ya bayyana sunan wanda ke daukan nauyin Kanu da Igboho cikinsu

Buhari mashirmanci ne, yana yaro lokacin da muka kwatowa Najeriya yanci, Ayo Adebanjo

Shugaban kungiyar Afenifere, Cif Ayo Adebanjo, ya caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan jawabin da yayi ranar 1 ga watan Oktoba ga yan kasa cewa Najeriya ba zata taba rabuwa ba.

Adebanjo ya ce ya kamata ace Buhari mai shekaru 78 da haihuwa ya fahimci cewa tattaunawa da yarjejeniya akayi kafin aka samu yancin kai a 1960.

A hirar da yayi da Jaridar Punch ranar Juma'a, Adebanji yace kodayake Buhari yaro ne a lokacin, bai san abinda ya faru ba.

Adebanjo wanda shekarun 93 yanzu ya kara da cewa irin wadannan kalamai na Buhari ke tayar da tarzoma.

Source: Legit.ng News

Online view pixel